✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tinubu da Atiku sun yi wa Obasanjo raddi kan goyon bayan Obi

APC da PDP sun ce ba su bukatar goyon bayan wani don lashe zabe a 2023.

’Yan takarar shugabancin kasa na jam’iyyun APC da PDP, Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar, sun yi wa tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo raddi kan ayyana goyon bayansa ga dan takarar Jam’iyyar Labour, Peter Obi.

Cikin sakon barka da sabuwar shekara da ya isar wa ‘yan kasa ranar Lahadi, Obasanjo ya ce idan aka kwatanta ‘yan takarar shugabancin kasa baki dayansu Obi ya fi sauran gwabi-gwabi ta fuskoki daban-daban.

Aminiya ta ruwaito cewa, Tsohon Shugaban ya ce babu daya daga cikin ’yan takarar shugabancin kasar da ba shi da kashi a gindinsa, amma idan za a kwatantasu ta fuskar ilimi da bin ka’ida da kuma irin ci gaban da za su iya kawowa Najeriya to Obi ya sha gaban kowa.

Don haka ya yi kira ga matasan kasar da su mara wa dan takarar na Jam’iyyar LP baya a daidai lokacin da ake tunkarar babban zaben kasar da za a yi a watan Fabrairu.

Obasanjo ya ce Tinubu da Atiku ba su ne zabin da ya dace da shugabancin Najeriya a wannan lokaci ba.

Tuni dai APC ta mayar wa tsohon Shugaban Kasar martani tana mai cewa mara wa Obi baya da ya yi ba zai taba zama barazana a gare ta ba.

A cewar Bayo Onanuga, Darektan Yada Labarai na Kungiyar Yakin Neman Zaben PDP,  mara wa Obi baya da tsohon Shugaban Kasar ya yi ba zai yi tasiri ba, “hasalima Obasanjo ba shi da wani tasiri ko amfani a siyasance a ko’ina a Najeriya da zai sa wani ya ci zabe.”

Ita ma kuma PDP ta ce da ma ba ta da bukatar goyon bayan kowa saboda kyakkyawan shirin da ta yi ya isa ya kai ta ga samun nasara a 2023.

Mai magana da yawun jam’iyyar, Debo Ologunagba, ya ce ‘yan Najeriya sun riga da karkata zuwa ga PDP da dan takararta, saboda haka wani mutum daya ba zai yi tasiri ba kuma hakan ko a habar zaninsu.

Kafin wannan lokaci, Tinubu da Atiku kowannensu ya ziyarci Obasanjo don tuntuba da neman tabarraki.