✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Tinubu ba zai wulakanta Kiristoci ba’

Abin fa na harkar siyasa ba haka yake ba.

Alhaji Abdullahi Musa shi ne Shugaban Kungiyar Arewa Dtra Network for Tinubu/Shatima 2023, reshen Jihar Kaduna.

A tattaunawarsa da wakilinmu, ya bayyana dalilin da ya sa Sanata Bola Tinubu ya dauki Kashim Shattima a matsayin wanda zai mara masa baya a takarar shugabancin kasa, a zaben badi.

Me za ka ce game da masu ce-ce-ku-ce, cewa Bola Ahmad Tinubu ba ya son mabiya addinin Kirista na Arewa, ganin ya dauki Musulmi a matsayin mataimakinsa a takarar zaben 2023?

Babu kamshin gaskiya ko kadan ga masu wannan magana, domin Sanata Bola Tinubu ya yi wa Kiristocin Arewa goma sha tara ta arziki tun kafin ya kai ga daukar Shattima a matsayin mataimakinsa.

A can baya, a 2015, lokacin da ya mara wa Shugaba Buhari baya ya ci zabe, nan take ya mika wa Shugaban sunan Babachir David Lawan, wanda Kirista ne dan kabilar Kilba daga Jihar Adamawa, don ya nada shi a mukamin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Kuma Buharin bai yi kasa a gwiwa ba ya nada shi a kan wannan babban mukami, har zuwa lokacin da aka same shi da aikata almundahana, aka sauke shi.

Bayan haka aka nada Boss Mustapha, wanda shi ma Kirista ne dan kabilar Kilba, duk ta sanadiyyar Tinubu.

To yanzu mutum mai irin wannan hali ne za a ce ba ya son Kiristoci? Kada fa mu manta, shi Tinubun nan matarsa Sanata Oluremi Kirista ce, amma yanzu saboda son zuciya na wasu mutane suna cewa wai Tinubu ya nuna wa Kiristoci bambanci saboda ya dauki Shattima a matsayin mataimakinsa a zabe mai zuwa.

Sannan wani abin mamaki cikin masu fadin wannan magana har da Babachir. To mun san halin mutum da mantuwa, watakila ya manta lokacin da Buhari ya tabbatar masa da mukamin Sakataren Gwamnatin Tarayyar, ya fito ya fada wa duniya cewa ba zai yi wa kowa godiya daga Arewa ba, sai dai ya gode wa Bola Tinubu, saboda shi ne ya sa Buhari ya ba shi mukamin.

To amma ba ka ganin kamata ya yi Tinubu ya dauki Kirista daga Arewa tun da shi Musulmi ne?

Abin fa na harkar siyasa ba haka yake ba. A kan maganar daukar Kashim Shattima, ina son in tunatar da Kiristocin Arewa cewa, siyasa ’yar lissafi ce.

Saboda haka, daukar Shattima ba yana nufin Tinubu ba ya son su ba ne, illa kawai dabara, domin kwashe wa PDP kafa.

Dalili ke nan ya dauke shi a matsayin mataimakinsa, kasancewarsa dan kabilar Kanuri wadanda suke da dimbin yawa a shiyyar.

Don haka ina kara jawo hankalin Kiristocin Arewa su san cewa Tinubu adalin mutum ne na kowa da kowa, wanda in ya ci zabe zai yi wa kowa adalci, ba tare da nuna bambancin addini ko kabilanci ko sashin da mutum ya fito ba.

Me za ka ce game da ’yan takarar jam’iyyarku ta APC a jiharku ta Kaduna?

Idan muka dawo jiharmu ta Kaduna, ina kiran al’umma su yi tururuwa ranar zabe, su zabi Sanata Uba Sani a matsayin Gwamnan Jihar.

Domin yayin da Malam Nasiru El-Rufa’i ya fi mai da hankali wajen sauya wa Kaduna fasali, ta wajen yin tituna da gadoji da gina sababbin kasuwanni, shi Malam Uba Sani in aka zabe shi, zai fi mai da hankali ne wajen gina al’umma, ta yadda kowa zai debi lagwadar dimokuradiyya.

Haka su ma ’yan takararmu na sanatoci a karkashin Jam’iyyar APC, wato Muhammed Sani Dattijo da Suleiman Abdu Kwari da Bulus Audu da ’yan takararmu na Majalisar Wakilai.

Irin su Bello El-Rufa’i da Muktar Ahmed Monrobia da sauransu, duk sun shirya tsaf, in aka zabe su, suka je majalisun, za su yi dokokin da za su amfani al’umma da kasa baki daya.

Za su kuma juyo gida, su rungumi talakawa, su tsoma hannayensu a cikin tukunyar romon dimokuradiyya kowa ya ji ana yi da shi.

Ina da kyakkyawan fata idan Allah Ya yarda, ’yan takararmu ba za su ba mutanen jiharmu ta Kaduna kunya ba.