Ga dukkan alamu hirar da gidan talabijin na ARISE ya yi da dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ta yi fami a kan gyambon siyasar kasar nan da bai gama warkewa ba game da dan daukar Musulmi Mataimakin dan takarar Shugaban Kasa a APC.
A cikin hirar Atiku ya ce Tinubu ya so Atiku ya dauke shi a matsayin mataimakinsa a zaben shekarar 2007 a karkashin tsohuwar Jam’iyyar AC, amma ya ki.
- Labaran Auratayya: Babana ne sanadin wahalar aurena!
- 1444 Hijiriyya: Muhimmanci da tasirin sabuwar shekara ga al’umma
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya ce sun raba gari da Tinubu ne bayan da ya gabatar da Ben Obi a matsayin mataimakinsa.
Ya ce: “Ya tsaya kai-da-fata mu yi takara tare, ban yi imani hakan daidai ne ba a samu tikitin Musulmi da Musulmi. Wannan shi ne babban dalilin rabuwarmu da shi.”
Ka tsufa amma kana shara karya — Tinubu
Sai dai a martanin da dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar APC, Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya mayar, ya ce Atikun ne da kansa ya dauke shi mataimakinsa kafin ya janye kamar yadda ya yi wa Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike a wannan karo.
A sanarwar da Kakakinsa, Tunde Rahman ya fitar, Tinubu ya ce, “abin bakin ciki ne mutum kamarsa ya rika shara karya.”
Ta ce Atiku “A kokarinsa na neman cin zabe ido rufe ta hanyar kawo bambancin addini ya zubar da mutuncinsa, inda ya kantara karya a gidan talabijin.”
Sanarwar ta ce dan takarar na PDP ya makance wajen neman shugabanci “don haka a shirye yake ya yi duk karyar da zai iya, da yake jin za ta sa ya samu ko da karin kuri’a daya ce.”
Tinubu ya kara da cewa: “Atiku yana son zama Shugaban Kasa. Sai dai iya abin da zai iya nunawa shi ne shi cikakken makaryaci ne. Duk wani batu na kare mutunci ya zubar.”
Ya bayyana yadda al’amura suka faru a zaben 2007 da cewa, Atiku ba ya cikin wadanda suka kafa Jam’iyyar AC, “Ainihin wadanda suka kafa jam’iyyar ce suka ba Atiku tikitin takara saboda bukatar da ke akwai ta a yaki kama-karyar da Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da PDP suka tsara a lokacin kan mulkin dimokuradiyya,” inji shi.
Ya ce, “A lokacin Obasanjo ya jingine ko ya yi waje da Atiku daga PDP. Muna bukatar hada hannu don yakar shirin mayar dakasar nan mai bin jam’iyya daya da Obasanjo ke son yi.
Atiku ya ci gajiyar wannan hadin hannu ne kawai ta a yaki maida kasa mai bin jam’iyya daya da PDP ta kaddamar.”
“Ina tausaya wa abokina Atiku duk da tsufarsa. Son cim ma burinsa ya dusashe alakarsa da gaskiya da amana kan abin da ya faru a baya. Mun kafa AC ce ba tare da saninsa ba.
A lokacin kusan Obasanjo ya kore shi daga PDP, don haka muka tallafe shi ta hanyar ba shi tikitin yin takara a zaben 2007.
“Bari in fadi baro-baro, Atiku ya ba ni tikitin mataimakin dan takarar Shugaban Kasa a zaben 2007. Kuma ina sake fadi, addinina bai canja ba. Lokacin da ya ba ni matsayin, ni Musulmi, kuma na yi imani yana sane da addinina a lokacin,” inji Tinubu.
Tinubu ya ce Atiku ya yi wa jama’a dungun ne kawai don jawo takaddama.
“Hakikanin hoton Atiku ya bayyana bayan shekara 15, ya yi wa Gwamna Nyesom Wike irin haka a wannan lokaci na zabe kuma ya saba. Wike Kirista ne.
“Don haka Atiku ba ya da hujjar kawo batun tikitin Musulmi da Musulmi in dai ba munafunci ba. Ya dauka mutane sun manta abin da ya yi ne a zaben 1993.
“Bayan ya fadi warwas a kokarinsa na neman tsaya wa Jam’iyyar SDP takara, me ya yi? Ya shiga nema tare da kamun kafa haikan fiye da kowa don ya zamo mataimaki ga Cif MKO Abiola.
“Idan Atiku zai ci gajiyar abu ba ya ganin laifi a yi tikitin Musulmi da Musulmi. Yana ganin komai daidai ne a irin wannan tikiti matukar zai ci gajiya.
“Yanzu Atiku na sukar zabin da na yi na mataimakin dan takara ta kafa hujja da addini. Idan Atiku zai fadi gaskiya ya san mutumin da na dauka a matsayin mataimaki ya fi cancanta da kujerar a kan wanda shi ya dauka.
“Don haka wannan mataki da muka dauka ba ya da nasaba da batun addini.Ya shafi dacewa da gogewa da karfin hali da hangen nesa ne,” inji Tinubu.
Cif Tinubu ya ce kafin ya dauki Shettima a matsayin mataimakinsa, ya saurari shawarwari tare da auna batun daidaito da kuma shawarwarin da ya samu daga dukkan ’yan Najeriya da suka damu da kasar nan.
Ya ce ya auna batun zaben Kirista da Musulmi kuma hujjojin kowane bangare sun dace, amma ba dama ya hada biyu duka, sai ya dauki abin da ya fi zama daidai kuma ake bukatarsa a halin da muka samu kanmu a yanzu da kuma ita kasar.
“A daukacin rayuwata game da mutanen da ke goya min baya ina lura da kwarewa da samar da dabaru da tausayawa da gaskiya da adalci da kuma yin abu bisa inganci,” inji shi.
Ya ce ba zai bar wannan salo ba domin ya taimaka masa lokacin da yake Gwamnan Legas inda ya samar da ingantacciyar gwamnati fiye da kowace jiha don haka yake son maimaita haka a matakin kasa don samar da Najeriya abar alfahari.
‘Neman mulki ido rufe ya sa ka wannan babatu’
A takarda ta biyu da Daraktan Labarai da Sadarwa na Kwamitin Kamfe na Tinubu (TCO) Mista Bayo Onanuga ya fitar, ya ce bayanan na Atiku a hirarsa da talabijin din cike suke da rashin gaskiya da kuma kura-kurai.
Ya ce, “Mun kalli hirar Atiku a gidan talabijin na ARISE kuma mun yi matukar kaduwa kan dimbin karairayi da jahilcin da dan takarar na PDP ya nuna.
A cikin hirar Alhaji Atiku ya nuna kansa a matsayin mutumin da bai shirya wa aikin da yake nema ba kuma mutumin da ba za a ba shi amanarmu ba.
“Ya rika kauce wa muhimman tambayoyin da aka yi masa a kan tarihin aikinsa da yadda ya tara dukiya a lokacin da yake aikin Kwastam. Ya murguda gaskiya ya shashantar da mutane.
Sanarwar ta ce, abu mafi firgici shi ne Atiku ya yi ikirarin keta doka a tsawon lokaci inda ya rika karya dokoki a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati.
“A matsayinsa na jami’in Kwastam a Idi-Iroko, Atiku ya ce ya rika tuka tasi, yana mai cewa “babu dokar da ta hana ma’aikaci yin kasuwanci a Najeriya.
“Mu kuwa mun gano hakan ba gaskiya ba ne. Duk wani ma’aikaci an wajabta masa ya kiyaye ka’idoji da dokokin aiki da suka hana ma’aikacin yin kasuwanci na kashin kai yayin da yake aikin gwamnati don hakan zai iya kawo cikas wajen aiwatar da aikin da aka ba shi.
“Tsarin Mulkin 1999 ya bayyana a Kashi na 1 Rataye na Biyar, Sashe na 2 (b) cewa, bai halatta ma’aikacin gwamnati in ba a wurin da aka dauke shi aiki ba, ya yi ko ya shiga a dama da shi wajen gudanar da wani kasuwanci na kashin kai, sana’a ko saye da sayarwa.
“Dokar ta amince ne kawai ma’aikaci ya yi noma.
“Muna mamaki wace doka Atiku ya dogara da ita wajen keta ka’ida a matsayinsa na ma’aikaci.
“Muna da ra’ayin cewa Atiku ya tauye doka a daukacin zamansa ma’aikacin gwamnati lamarin da ya jawo ya kafa Kamfanin Intel Logistics tare da marigayi Shehu ’Yar’aduwa da wasu Italiyawa, duk da cewa yana aikin gwamnati a matsayin ma’aikacin Kwastam.
Sauran wuraren da kwamitin ya soki Atiku a kai sun hada da rashin sanin manyan ginshikan tattalin arziki da gabatar da bayanan karya kan Masar cewa kasar tana da ’yan sanda miliyan biyu da suke kula da mutum miliyan 80, maimakon ’yan sanda dubu 500 da suke kula da mutum miliyan 104.
Sai kuma da aka tambaye shi dalilin da PDP ta yi watsi da Sashe na 3 (c) na tsarin mulkinta kan karbakarbar takarar Shugaban Kasa, ya kama bayani a kan Wike da kokarin da yake yi wajen sulhu da shi.
“Sannan da yake wasa da hankalin jama’a kan tikitin Musulmi da Musulmi ya kasa ganin cewa bai kamata ya nemi takara ba, bayan Shugaban Kasar da ke kai da ya shafe shekara 8 ya fito ne daga yankinsa,” inji sanarwar.
Ta ce Atiku ya rika tufka da warwara wajen bayar da amsa inda a wani wurin ya ce karba-karbar mulki ba ya cikin tsarin mulki.
Kuma a wani wurin ya ce PDP ba ta tsara karba-karbar wani matsayi ba. Kuma daga baya ya ce jam’iyyar tanakarba-karbar mulki a tsakanin Kudu da Arewa.
Martaninku abin dariya ne —Atiku
Sai dai bangaren Atiku ya ce ya yi dariyar abin da ya kira “gwamen” martani da Kwamitin Kamfe na Tinubu ya mayar.
Wata sanarwa daga Kakakin Atiku, Paul Obe ta kuma kalubalanci Tinubu ya fito ya yi irin wannan tattaunawar.
Sanarwar ta ce, “Mun yi dariyar karanta gwamen martanin Kwamitin Kamfe din Tinubu kan doguwar tattaunawar da Waziri Atiku Abubakar ya yi da gidan talabijin na ARISE a ranar 21 ga Yuli, 2022.
“Abin dariyar shi ne mun san Tinubu ba zai iya zama ya tattauna ta dogon lokaci ba saboda wasu dalilai.
“’Yan Najeriya suna ganinsa yana magana a bainar jama’a kuma sun san dalilin da ba zai iya yin haka ba,” inji sanarwar.
Daga nan sai ya dauki batutuwan da Kwamitin TCO ya bijiro da su ya warware su daya bayan daya inda ya ce, abin da Atiku ya yi a lokacin yana matashin ma’aikacin Kwastam bai saba wa doka ba, kuma ya kamata Kwamitin TCO ya fahimci cewa Najeriya ba a karkashin mulkin soja take ba, kuma tsarin mulki ba zai koma baya ya yi hukunci kan abin da aka yi kafin shi ba.
Game da batun karba-karba, ya ce: “Ga alama Kwamitin TCO (kwamiti ne da ba kintsattse ba da za mu kira kintsattse?), wanda bai san ma’anar karba-karbar mulki ba da kuma raba mukamai a tsakanin shiyyoyi ba.
“Don haka muna farin cikin ilimantar da su. Karba-karbar mulki na nufin tanadin tsarin mulki na karbakarbar mulki a tsakanin Kudu da Arewa.
“Yayin da raba mukamai a tsakanin shiyyoyi yake nufin abin da ba tsari ne na kundin tsarin mulki ba, a tsakanin shiyyoyin siyasa shida.
“Muna fata wannan zai magance jahilcin siyasa na marubuta waccan takarda,” inji bangaren Atiku.
Sanarwar ta yi watsi da zargin karanci ilimi ga Atiku inda ta ce yana da digiri na biyu daga Jami’ar Angah Ruskin, kuma tana kalubalantar dukkan ’yan takarar Shugaban Kasar su gabatar da takardar ilimi kamarta ko wadda ta fi ta.
Kuma ta ce duk mai so yana iya tuntubar jami’ar don tantance wannan da’awa.
‘In ka isa ka je ka yi hirar awa daya kama ta’
“A karshe muna kalubalantar Bola Tinubu ya je a tattauna da shi ta awa daya kamar yadda Waziri ya yi, inda zai iya bayyana manufa da nuna kwarewa kamar yadda dan takararmu ya yi, a nan ne zai iya yin magana.
“Idan ba haka ba, muna sanar da shi da ’yan ma’abbansa cewa ba su da ikon nuna wa wasu yatsa matukar ba za su iya zama a kujerar tattaunawar ba,” inji sanarwar.
A hirar dai Atiku ya ce ya dauki Gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa ne don shi ne wanda zai iya cin zabe da shi, kalaman da suka tunzura bangaren Gwamnan Ribas Nyesom Wike.
Sai dai Wike ya ce zai yi magana a kan wannan batu a nan gaba, a daidai lokacin da magoya bayansa suke caccakar hirar tare da nuna cewa hakan alama ce ta rashin neman maslaha daga bangaren Atikun.