✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tifar yashi ta muttsuke mata 6 har lahira a Maiduguri

Wata tifa ta muttsike akalla mata shida har lahira a unguwar Kaswan Fara da ke Shagari Lowcost a garin Maiduguri, ranar Juma'a.

Wata tifa makare da shayi ta muttsike akalla mata shida har lahira a unguwar Kaswan Fara da ke Shagari Lowcost a garin Maiduguri, ranar Juma’a.

Wani ganau, Kola Fatai ya ce tifar ta bi ta kan wata a-kori-kura da ke dauke da mutane, nan take ta kashe mata shida wasu da dama kuma suka samu rauni.

Ya bayyana cewa mutanen sun gamu da ajalinsu ne bayan burkin motar ya tsinke a daidai lokacin da take dauke da yashi a kan hanyar Gubio da ke wajen garin Maiduguri da misalin karfe 10 na safe.

Wani mazaunin unguwar mai suna, Iman Buba ya shaida wa wakilinmu cewa fusatattun matasa sun banka wa wasu tifofi biyu wuta sakamakon faruwar hatsarin.

A cewarsa, yawan matan da suka rasu a hatsarin sun kai goma, wanda ya sa masu zanga-zangar tare hanyar Maiduguri zuwa Gubio.

Wani shaida ya ce tifar da ta kashe matan tana kokarin shan gaban wata tifa ne, amma ta kwace ta hau kan a-kori-kurar da matan suke ciki.

Tuni aka tura jami’an tsaro zuwa wurin domin kwantar da tarzomar.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Borno, ASP SK Shatambaya, amma ya ce masa ba su samu rahoto ba.