Sama da mutum miliyan 10 ne suka bude shafinsu a sabon dandalin Threads, wanda Meta, mamallaka shafin sada zumunta na Facebook suka kirkira don ya zama kishiyar Twitter.
Mamallakin kamfanin na Meta, Mark Zuckerberg ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis.
- Kotu ta bayar da belin Abba Kyari bayan wata 18 a gidan yari
- Tinubu ne da kansa zai bayyana sabuwar ranar da za a yi kidayar jama’a – NPC
Sabon dandalin dai ya fara aiki ne a kasashe fiye da 100 da misalin karfe 12:00 na safiyar Laraba a agogon Najeriya da Nijar, kuma yanzu haka ana iya sauke shi a kan wayoyin Apple da Android.
Sai dai an samu tsaikon sakin shi a kasahen Turai, saboda batutuwan da ke da jibi da kare hakkin masu amfani da intanet.
Ana sa ran dandalin zai kasance babbar kishiya ga Twitter, wanda a dan tsakanin nan shafuka da dama ke barazanar kwace mata mabiya, kodayake ba su kai ga yin hakan ba.
Ga wasu abubuwa biyar da ya kamata ku sani a kan wannan sabon dandali:
- Masu amfani da shafin za su iya rubutu da haruffa har guda 500, kuma yana da abubuwa da dama masu kamanceceniya da shafin Twitter.
- Ko da mutum ya goge shafinsa a kan dandalin, hakan ba zai shafi shafinsa na Instagram ba.
- Duk dan shekara 12 zuwa sama zai iya bude shafi a cikinsa, kuma za a same shi a harsuna fiye da 31, ciki har da Ingilishi da harsunan kasashen China da Rasha da Spaniya.
- Babu wahalar bude shafi a dandalin; za ka iya budewa da bayanan shafinka na Instagram. Zai taho da dukkan bayananka da suke can, sannan za ka iya yin gyara domin su dace da shi.
- Dandalin zai dauki tsaron masu amfani da shi da muhimmanci, sannan zai tabbatar ana bin dokokin amfani da shafi, irin na Instagram, sau da kafa.