✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Thomas Tuchel ya fara aiki gadan-gadan a Chelsea, Di Maria zai koma Tottenham, Haaland zai tafi Chelsea

Sabon Kocin da a ranar Talata ya karbi ragamar jagorancin horas da ’yan wasan Chelsea Thomas Tuchel, ya kama aiki gada-gadan inda a daya daga…

Sabon Kocin da a ranar Talata ya karbi ragamar jagorancin horas da ’yan wasan Chelsea Thomas Tuchel, ya kama aiki gada-gadan inda a daya daga cikin tsare-tsarensa na farko yake shirin dauko dan wasan RB Leipzig na kasar Faransa mai shekaru 22, Dayyot Upamecano. SportBild

Dan wasan Borussia Dortmund na kasar Holland mai shekaru 20, Erling Haaland, shi ne dan wasa na farko daTuchel yake so Chelsea ta zuba kudi wajen daukarsa. The Sun

Tottenham ta soma tuntubar PSG kan yiwuwar dan wasanta na kasar Faransa mai shekaru 32 Angel di Maria wanda zai samu damar barin kungiyar a bazara. L’Equipe via Talksport

PSG ta ci gaba da tuntubar Tottenham domin samun damar karbar aron dan wasanta na Ingila, Dele Alli a watan Janairu inda Tottenham take duba yiwuwar daukar dan wasan Borussia Monchengladbach na kasar Jamus, Florian Neuhaus a matsayin wanda zai maye gurbinsa. Mirror

West Ham ta samu kwarin gwiwar a kan dan wasanta mai shekaru 22 Declan Rice, bisa tunanin Chelsea za ta daina zawarcinsa bayan sallamar da ta yi wa kocinta Frank Lampard a ranar Litinin. Telegraph

Ana hasashen kafin sallamarsa, Frank Lampard ya kudiri aniyar sayar da wasu ’yan wasan Chelsea biyar domin tattara kudin da kungiyar za ta samu damar dauko dan wasan na kasar Ingila. Express

Akwai yiwuwar dan wasan Belgium Christian Benteke, zai ci gaba da zama a Crystal Palace duk da zawarcinsa da West Bromwich Albion ke yi. Sky Sports

Arsenal za ta fafata da Barcelona wajen daukar dan wasan Manchester City na kasar Sifaniya mai shekaru 21, Eric Garcia wanda ke shirin barin kungiyar a bazara. Mundo Deportivo

Tottenham tana zawarcin dan wasan Napoli na kasar Serbia, Nikola Maksimovic mai shekaru 29, a yayin da kwataraginsa zai kare a karshen kakar wasannin bana. Spazio Napoli

Everton na fafatawa da Parma a yunkurin daukar dan wasan Bayern Munich, Joshua Zirkzee mai shekaru 19, inda ake has ashen Everton ta nemi karbar aron dan wasan wanda kuma a yarjejeniyar da take son kullawa akwai  zabin sayensa a kan Fam miliyan 8.9. Sky Germany