✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Thierry Henry ya yi ritaya a kwallon kafa

Tsohon dan kwallon kulob din Arsenal da ke Ingila kuma haifaffen Faransa da ake wa lakabi da “Igwe” Thierry Henry a ranar Litinin da ta…

Tsohon dan kwallon kulob din Arsenal da ke Ingila kuma haifaffen Faransa da ake wa lakabi da “Igwe” Thierry Henry a ranar Litinin da ta gabata ne ya yi ritaya daga buga kwallo a wata sanarwar da ta fitar.

Thierry Henry dai ya shafe kimanin shekara 20 yana buga wasan kwallo kuma ya yi wasa a kulob da dama da suka hada da kulob din Monaco da na Jubentus da ke Faransa da FC Barcelona a Sifen da na Arsenal a Ingila da kuma na New York Red Bulls da ke Amurka.
dan shekara 37, Henry yana daya daga cikin ’yan kwallon da suka lashe wa kulob din Faransa gasar cin kofin duniya a shekarar 1998.
Sai dai yayin da Henry ya bar kwallo zai cigaba da aiki ne da kafar sadarwar wasanni ta Sky Sports inda zai zama daya daga cikin masu gabatar da sharhin wasan kwallon kafa.
Theiry Henry dai ya samu nasarar zuwa kwallaye 175 a raga a gasar rukunin firimiya na Ingila al’amarin da ya sa ya zama na hudu a jerin wadanda suka fi zura kwallaye a raga a gasar.
Daga cikin nasarorin da ya samu a kwallon kafa sun hada da nasarar lashe kofunan gasar firimiya na Ingila har sau biyu da kuma kofin kalubale (FA) a kulob din Arsenal a wasannin da ya yi wa kulob din a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.
Haka kuma ya samu nasarar lashe kofin zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) da kulob din FC Barcelona na Sifen a shekarar 2009.
Ya sake komawa kulob din Arsenal na Ingila a shekarar 2012 a matsayin na wucin gadi inda ya samu nasarar zura kwallo a ragar Leeds a wasa zagaye na uku na kofin kalubale na Ingila.
Sannan Thierry Henry ne dan kwallon da ya fi zura wa Faransa yawan kwallaye a raga kuma a shekarar 1994 ne ya taimaki kulob din Monaco na Faransa wajen lashe kofin gasar rukunin Faransa (Ligue 1).
Sai dai masana harkar kwallo sun yi hasashen Thierry Henry yana da burin ya zama kocin kulob din Arsenal a nan gaba.