✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Theresa May  ta tsallake rijiya da baya

Firayi Ministan Birtaniya Misis Theresa May ta tsallake rijiya da baya a kuri’ar da Majalisar Dokokin Kasar ta kada don nuna rashin gamsuwa da salon…

Firayi Ministan Birtaniya Misis Theresa May ta tsallake rijiya da baya a kuri’ar da Majalisar Dokokin Kasar ta kada don nuna rashin gamsuwa da salon mulkinta a shekaranjiya Laraba da dare.

Firayi Ministan ta samu  kuri’a 200 na wakilan majalisar da suka goya mata baya, yayin da wakilai 117 suka nuna rashin gamsuwa da salon mulkinta.

Jefa kuri’ar ta biyo bayan nuna bukatar haka da wakilan jam’iyyarta 84 a majalisar da suka fusata da shirinta na ficewa daga Tarayyar Turai, wanda suka ce ya saba wa sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta shekarar 2016.

Firayi Ministan ta ma zarce zuwa birnin Brussels don halartar taron Tarayyar Turai (EU) a jiya Alhamis da safe bayan tsallake kuri’ar.

Za ta bukaci a yi aiki da alkawarin da shugabannin kasashen Tarayyar  Turai suka yi kan matsayar yankin Ireland – wani babban abin da ke kawo cikas ga wakilan majalisar da suke adawa da shirinta na fitar da Birtaniya daga Tarayyar Turai.

Tarayyar Turaia dai ba za ta warware yarjejeniyar ba, amma tana iya bayar da babban tabbaci na wucin-gadi kan matsayar kamar yadda Sashin Ingilishi na BBC ya ruwaito.

Da take jawabi a fadarta da ke Titin Downing Street bayan kada kuri’ar Misis May ta sha alwashin tabbatar da ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai “da jama’ar kasar suka zaba” to amma ta ce ta saurari damuwar wakilan majalisar da suka jefa kuri’ar nuna rashin gamsuwa da salonta.

Jagoran Jam’iyyar  Liberal Democrat mai matsakaicin ra’ayi, Mista Bince Cable ya ce duk da ‘gagarumar tirka-tirkar’ ta ranar Laraba, “babu wani abin da ya canja.”

Tsohon jagoran jam’iyyar Mista Iain Duncan Smith ya ce ya rage ga Misis May ta saurari jam’iyyarta kuma “ta tunkari Tarayyar Turai…. Don warware takaddamar.”

A taron na jiya, Misis May za ta samu damar gabatar da matsalolin gaba-da-gaba ga dukkan shugabannin kungiyar 27.

Kuma shugabannin za su duba abin da za su iya yi ba tare da Misis May tana cikin dakin taron ba.