Firayi Ministar Birtaniya Misis Theresa May ta sanar da mafita game da batun yarjejeniyar fitar kasarta daga Tarayyar Turai da ake kira da Bredit a takaice, inda ta ce lallai akwai bukatar Majalisar Dokoki ta amince da yarjejeniyar ta Bredit.
Misis May a yayin ganawa da wakilan jam’iyyu ta ce, tattaunawar da aka yi ta zama mai ma’ana matuka, kuma babbar hanyar barin yarjejeniyar Bredit a waje daya ita ce, majalisar ta amince da yarjejeniyar wadda ita ce manufar gwamnati a yanzu.
Ta ce, hanyar watsi da Bredit ita ce a amince da yarjejeniyar fasa fita daga Tarayyar Turai gaba daya.
Firayi Ministar ta ce a ranar 29 ga Janairu za a jefa kuri’a a kan sabon kudirin da za a mika ga Majalisar Dokokin Kasar.