✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tella: Kasuwar da ake cinikin sama da shanu 3,000 a rana daya

Tan daya daga cikin manyan kasuwannin shanu a Arewa maso Gabas

Kasuwar Shanu ta garin Tella a Karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba daya ce daga cikin manyan kasuwannin shanu a Jihar da kuma Arewa maso Gabas.

Wannan babbar kasuwar tana gudana ce a kowace ranar Lahadi, kuma ana kawo shanu daga sassan jihar da wasu jihohi na kasar nan har ma da kasar Kamaru.

Binciken da wakilin Aminiya ya gudanar a kasuwar ya gano cewa dubban masu saye da sayar da shanu ne suke gudanar da kasuwanci a wannan babbar kasuwa.

Daruruwan masu sayen shanu daga sassan kasar nan da suka hada da jihohin Kano da Bauchi da Filato da Babban Birnin Tarayya, Abuja da kuma jihohin Kudu maso Gabas ne suke zuwa kasuwar don sayen shanu a kowane mako.

Aminiya ta gano cewa ana sayar da shanu fiye da dubu uku a kowace ranar kasuwar. Har wa yau akwai jama’a musamman matasa masu yawan gaske wadanda suke samun kudi a kasuwar ta hanyoyi daban-daban kamar sa shanun a motoci da sauke su daga motocin da suka kawo su daga kauyuka da garuruwa.

Akwai kuma direbobin manya da kananan motoci da suke jigilar shanu daga kasuwar zuwa sassan kasar nan da suke samu kudin shiga masu yawan gaske.

Binciken Aminiya ya nuna cewa ana samun shanu a kan farashi mai sauki fiye da sauran kasuwanin shanu da ke jihar da wasu kasuwanni da ke jihohi makwaftaka da jihar.

Saukin farashin shanu a Kasuwar Tella yake sa masu harkar shanu suke zuwa kasuwar a kowane mako, inji wani falken shanu mai suna Alhaji Shu’aibu Sa’idu. Ya ce farashin shanu yana kamawa daga Naira 70,000 zuwa Naira dubu 500 ko dubu 700.

Alhaji Shu’aibu Sa’idu ya ce a wasu lokuta ma ana samun saniyar da ake sayarwa a kan Naira miliyan daya.

Sarkin Turken Kasuwar, Malam Julde Aboki ya shaida wa Aminiya cewa Kasuwar Tella tana daya daga cikin manyan kasuwanni shanu a Jihar Taraba.

Ya ce ana sayar da shanu manya da kananan sama da dubu uku a duk ranar kasuwa.

Sarkin Turken ya kara da cewa Kasuwar Tella tana da matukar amfani ga jama’a da kuma gwamnatin jihar da karamar Hukumar Gassol ta hanyar samar da kudaden shiga.

Ya ce matasa masu yawan gaske na samun kudade ta fuskar saye da sayar da shanu da maganin dabbobi har ma da lodi da sauke yi ga motocin da suka kawo shanu daga kauyuka da garuruwa.

Ya ce ba Fulani ne kawai ke kawo shanu kasuwar ba, har ma da sauran wadanda ba Fulani ba. Sarkin Turke Aboki ya ce harkar kiwon shanu harka ce da jama’a suka dauka gadan-gadan saboda ribar da ake samu.

Alhaji Julde Aboki ya ce a duk ranar kasuwa akwai matashin da ke samun Naira dubu 50 ko fiye a matsayin ribar saye da sayar da shanu.

Ya ce Gwamnatin Jihar Taraba da karamar Hukumar Gassol na samun kudade shiga da masu saye da sayar da shanu a kasuwar ke biya.

Sarkin ya koka dangane da rashin kula da kasuwar da gwamnati ke yi duk da yawan kudaden shiga da take samu a kasuwar.

Ya ce akwai bukatar a kewaye kasuwar don inganta tsaro tare da gina rumfuna inda ’yan kasuwa za su fake a lokacin da ake ruwan sama ko lokacin tsananin zafin rana.

Alhaji Julde Aboki ya kuma nemi gwamnatin jihar ta taimaka a samar ta banki a kasuwar musamman da yake ana gudanar da hada-hadar kudi masu yawa a cikinta.

Ya ce akwai bukatar samar da karamin asibitin dabbobi a kasuwar domin kula da shanun da ake saye da sayarwa.

Shi ma da yake magana a kan kasuwar, wani falken shanu mai suna Adamu Buba Chukka ya ce a duk ranar kasuwa yana sayen shanu sama da 200.

Ya ce ya dauki tsawon lokaci yana harkar sayen shanu kuma kasar lbo yake kai su don sayarwa.

Ya ce a halin yanzu farashin shanu ya tashi sosai inda duk wanda yake kasuwancin shanu ya zame masa tilas ya nemi jari mai gwabi.

Adamu Chukka ya ce a shekarun baya falken shanu ba ya bukatar jari mai yawa kafin ya fara wannan harka.

Kuma ya ce a shekarun baya ana samun babban sa wanda kudinsa bai wuce Naira dubu saba’in ba.