✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

TB Joshua: Fitaccen mai wa’azin Kirista ya rasu

Fitaccen mai wa'azin Kirista, Fasto TB Joshua ya yi mutuwar fuju'a.

Majami’ar ‘Synagogue’ ta tabbatar da rasuwar shugabanta, Fasto Temitope Balogun Joshua wanda aka fi sani da TB Joshua.

Rahotanni sun bayyana cewa Fasto TB Joshua ya rasu ne da yammacin Asabar jim kadan bayan kammala wani wa’azi a cocinsa da ke Jihar Legas.

  1. Yadda za a magance rashawa a Najeriya —Shugaban Media Trust
  2. Dubun manomin da ya zuba guba a rijiyoyi 9 ta cika

Har yanzu babu cikakken bayani game da abin da ya yi sanadin rasuwar mai wa’azin, wadda ta zo cikin wani yanayi na bazata.

Mamacin mai wa’azi ne da ya yi fice a Najeriya da ma wasu kasashe a fadin duniya kuma ya kasance mai taimakon jama’a ne.

An haifi Fasto TB Joshua a ranar 12 ga Yuni, 1963, kuma a lokacin rayuwarsa shi ne Shugaba kuma wanda ya assasa majami’ar ‘The Synagogue, Church of All Nations (SCOAN)’, cokcin da ke kula da gidan talabijin na Emmanuel da ke Jihar Legas.