Tawagar kwarru da aka dora wa alhakin binciken gano tushen annobar coronavirus ta isa birnin Wuhan na kasar China inda cutar ta fara bulla.
Kwararrun na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun isa birnin Wuhan ne a ranar Alhamis bayan sa-to-sa-katsin da ya kawo wa ziyarar tasu tarnaki.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa ’yan Kasuwar Kantin Kwari 18 a hanyar Aba
- Nuna tsiraici: Fatima Ribadu ta nemi afuwa
- An cafke Matashin da ya yanke wa ’yar shekara 6 mafitsara a Bauchi
- Dalilin da ya sa na bude gidan abinci- Fati Bararoji
Saukar masu binciken ke da wuya, aka yi musu gwajin cutar ta coronavirus sannan aka killace su sai bayan mako biyu.
Kwararrun za su yi aiki tare da masu binciken kimiyya na kasar China a aikin gano tushen kwayar halittar cutar.
A shekarar 2019 aka fara gano bakuwar kwayar coronavirus wadda ke haddasa cutar COVID-19 a birnin Wuhan na China.
Binciken gano asalin kwayar cutar na da hadari a siyasance, inda China ke gudun a dora mata laifin barkewar annobar COVID-19 da ta addabi duniya.
Amma masana kimiyya a kasar sun jima sun tababa ko a kasar cutar ta fara bulla, suna ganin akwai yiwuwar a wasu kasashen ta fara bulla kafin daga baya a gano ta Wuhan.
Sun ce alamun kwayar cutar da aka gano a kan wasu kayan kankara da aka shigo da su daga kasashen ketare na iya zama shaida cewa daga kasashen waje aka shigo da kwayar coronavirus a Wuhan.
Amma masu bincike na zargin jemagu daga yankin Kudancin China ne suka fara yada cutar.