✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tawagar Shugaban Kasa ta je ta’aziyyar Dokta Ahmad Bamba

Sheikh Pantami ne ya jagoranci tawagar da ta je jajanta wa daukacin al’ummar Kano.

Tawagar Shugaban Kasa ta je ta’aziyyar bajimin malamin addinin Islama kuma masanin Hadisi, Dokta Ahmad Ibrahim Muhammad da ya riga mu gidan gaskiya a ranar Juma’a.

A ranar Asabar ce Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami ya jagoranci tawagar da ta je jajanta wa daukacin al’ummar Kano da kuma Musulmi dangane da wannan babban rashi da aka yi.

Da yake gabatar da ’yan tawagar, mai magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya aiko su domin su jajanra wa iyalan mamacin da kuma jama’ar Kano baki daya.

Jagoran tawagar, Sheikh Pantami, ya ce mutuwar fitaccen malamin babban rashi ne ga kasa baki daya, yana mai cewa mutuwarsa ta bar babban gibi da ba za a iya cike shi ba.

Ya addu’ar cewa Allah Ya sanya Aljannah ce makomarsa, sannan kuma Ya bai wa iyalansa, dalibansa, da sauran abokan huldarsa juriyar wannan rashi da suka yi.

A nasa jawabin da ya yi a madadin abokanan huldar mamacin, Babban Limamin Masallacin Jami’ar Bayero da ke Kano, Dokta Abubakar Jibrin, ya yi godiya ga shugaban kasa da kuma tawagar da ya aiko dangane da wannan ziyara.

Dubun dubatar mutane ne suka halarci jana’izar fitaccen malamin addinin Musuluncin.

An dai binne malamin, wanda ya rasu ranar Juma’a a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH), a makabartar Dandolo.

Sheikh Bamba kamar yadda wasu ke kiransa, ya shahara da gudanar da Tafsirin Alkur’ani da Hadisai a Masallacin Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) da kuma makarantarsa ta darul Hadith da ke unguwar Tudun Yola a cikin birnin Kano.

Marigayin, wanda ya rasu yana da shekara 82 a duniya, yana cikin malaman Musulunci masu fada a ji a ciki da wajen Kano.

Ranar Lahadi ne ya yi karatunsa na karshe, har ma ya sanar da hutu na dan wani lokaci, saboda yanayin jikinsa.

Dokta Bamba tsohon malami ne a Sashin Nazarin Harshen Larabci a Jami’ar Bayero da ke Kano, wanda ya ajiye aikin ya kuma dirfafi harkar da’awa da wa’azi gadan-gadan.

A shekarun baya, ana kiran malamin da sunan “Kala Haddasana”, wani lakani da masu halartar karatunsa musamman wanda ya shahara a kai na littafin Muwadda Malik suka sanya masa.

Bayanai sun ce dan asalin kasar Ghana ne kuma a can aka a haife shi.

A wata tattaunawa da wani dansa ya yi da manema labarai, ya ce mahaifinsa “ya dawo Najeriya ne bayan da ya yi karatun digirinsa a Saudiyya, sai ya koma Najeriya ya fara koyarwa a Jami’ar Bayero ta Kano har ya yi digirin-digirgir.

Bajimin malamin ya bar yara 28 zuwa 30 kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana.