✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taurarin Zamani: Muhammad Usman ‘Razaki Dadin Kowa’

Razaki ya ce har yanzu Kannywood jaririya ce ta bangaren samun kudi idan aka kwatanta da Hollywood da Bollywood.

Matashin jarumi, Muhammad Usman wanda aka fi sani da Razaki a cikin shirin ‘Dadin Kowa’, ya bayyana cewa masana’antar Kannywood ta ci gaba ta bangaren kayan aiki da kuma fina-finan da take yi, idan aka kwatanta da shekarun baya.

Sai dai ya ce duk da haka, har yanzu masana’antar jaririya ce ta bangaren samun kudi idan aka kwatanta da Hollywood da Bollywood.