✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taurarin Zamani: Abba Ali Zaki

Jarumin bayyana takaicinsa kan yadda 'yan wasu yankuna ke zuwa Arewa su ci Kannywood da yaki, inda suka shirya fina-finai da labarin Bahaushe, kuma fin…

Matashin jarumi a Kannywood, Abba Ali Zaki, ya ce yawancin furodusoshin masana’antar karensu bai kai tsaiko ba, bare har su shirya fim, shi ya sa ake da karancin fina-finan da suka amsa sunansu a masana’antar.

Abba ya kuma bayyana takaicinsa kan yadda ‘yan wasu yankuna ke zuwa Arewa su ci Kannywood da yaki, inda suke shirya fina-finai da labarin Bahaushe, kuma fim dinsu ya fi na Kannywood kawo kudi.