✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taurarin Amurka 4 masu sarautun gargajiya a Najeriya

Ga wasu manyan taurarin Amurka da ke rike da sarautun gargajiya a Najeriya.

A yayin da ake bikin zagayowar Watan Tarihin Bakar Fata ta bana, Aminiya ta rairaiyo wasu manyan taurarin Amurka da ke rike da sarautun gargajiya a Najeriya.

Ga wasu daga cikinsu:

Jay-Z

Jay-Z, wanda shahararren mawakin gambara ne kuma marubuci, yana rike da sarautar Sarkin Wakan Ilon, wanda Masarautar Ilori ta ba shi a shekrar 2006.

Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Gambarita, ya yi wa Jay-Z nadin ne a lokacin da shararren mawakin tare da matarsa Beyoncé Knowles, suka ziyarci Jihar Kwara domin bude da aikin samar da ruwan sha da gwamna jihar na lokacin, Bukola Saraki ya yi.

A lokacin ne kuma aka nada wa wani titi suna Shawn Jay Z Carter a birin Ilori. Sunan Jay-Z na asali shi ne Shawn Corey Carter.

Danny Glover

Jarumin fina-fanan Amurka kuma dan gwagwarmayar siyasa, Daniel Lebern Glover wanda aka fi sani da Danny Glover, ya samu sarautar gargajiya a Najeriya.

An nada Danny Glover ne a matsayin “Enyioma of Nkwerre” a Masarautar Imo a ranar 6 ga watan Afrilun, 2009.

Forest Whitaker

Wani fitaccen jarumin fim kuma furodusa a masana’antar fim din Amurka, Forest Steven Whitaker, na daga cikin fitattun Amurkawa masu sarauta a Najeriya.

An gano cewa kakannin kakanninsa ’yan asalin yankin Nkwerre ne a Jihar Imo ta Najeriya.

Ya sha ziyarartar Najeriya, inda ziyarar da ya kawo a 2009 aka ba shi sarautar “Nwannedinamba of Nkwerre”.

James Guyton

Shi ma mawaki James Guyton, yana cikin jerin taurarin Amurkawa masu sarauta a Najeriya inda yake da sarautu biyu.

Shi ma mawakin ya gano cewa zuri’arsu ta fito ne daga Jihar Abia, inda Sarkin Yankin Ofeme da ke Karamar Hukumar Abiya ta Arewa, Eze E.C.O Udoka, ya nada shi a matsayin “Nwannedinamba of Ofeme” a sheakrar 2020.

Baya ga sarautar, an rada wa makwakin suna Chiwetara da harshen Igbo.