Sanya kambu da guru da laya da makamantansu don dauke wata cuta ko tunkudeta, shirka ne Allah Ya ce, “Ku b ani labarin abin da kuke kira ba Allah ba, yanzu idan Allah Ya nufe ni da wani ciwo za su iya warkar da ni, ko Allah Ya nufe ni da wata rahama da za ta same ni, shin za su tare wannan rahamar ba za ta same ni ba? To ka ce, ni dai Allah ne madogara na kuma gareShi duk masu dogara suke dogara.” (Zumar, 38).
An ruwaito daga Imrana dan Husaini (R.A) ya ce, Annabi (S.A.W) ya ga wani mutum sanye da kambu na farin karfe sai Annabi ya ce, “mene ne wannan?” Sai ya ce ai maganin shawara ne. Sai Annabi ya ce, “To cire ta, ba za ta kara maka komai ba sai rauni. Kuma wallahi da ka mutu da wannan kambun a jikinka da ba ka da rabo har abada.” (Imam Ahmad ya ruwaito).
An samu wani Hadisi daga Ukbata dan Amru shi kuma ya karbo daga Annabi (S.A.W). Annabi ya ce, “Wanda ya rataya laya, to kar Allah ya biya masa bukatarsa. Wanda kuma ya rataya wuri, kar Allah Ya yi masa maganin abin da ya rataya dominsa”. A wata ruwaya Annabi cewa ya yi, “Duk wanda ya rataya laya to ya yi shirka da Allah” kamar yadda aka samu daga Abi Hatim shi kuma daga Huzaifa; wata rana ya ga wani mutum yana sanye da zare wanda aka yi guru da shi wai maganin zazzabi, sai ya tsinke wannan zaren, sai ya karanta masa ayar Al-kur’ani inda Allah Yake cewa, “Yawancin wadanda suka yi imani da Allah sai a same su kuma suna shirka da Allah.” (Yusuf, 106).
Babi Na Takwas
Tofi, Laya da Rubutun Sha An samu Hadisi daga Bukhari wanda Abi Bashir (R.A) ya ruwaito, ya kasance tare da Annabi a daya daga cikin tafiye – tafiyensu. Sai Annabi Ya zabi wani mutum guda ya ce masa, kar ya bar wani rakumi da abun wuya har sai ya tsinke shi. Ita kuma ruwayar Ibn Mas’udu ga abin da ta ce: Annabi ya ce, “Tofi da laya da rubutun sha shirka ne.” (Ahmad da Abu Dawud suka ruwaito).
Laya: Wani abu ne da ake ratayawa yara don tsoron sammu. Wadansu malamai sun ce idan an rubuta ayar Alkur’ani ne, to abin da dan sauki. Amma wadansu suka ce ko da Alkur’ani ne, bai halatta ba saboda shirka ne, kuma Ibn Mas’ud yana daga cikin wadanda suka ce shirka ne.
Tofi: Shi ne addu’o’i wadanda wasu hujjoji sun halatta su idan dai babu shirka a ciki (kamar sunayen Mala’iku ko Annabawa ko Aljannu ko Waliyyai). Idan aka yi da sunayen wadannan to an yi shirka. Idan ba wadannan ba ne to Annabi (SAW) ya yi sauki a waje biyu kambun baka da dafi.
Rubutun Sha: Shi kuma wani abu ne da mata suke nema a yi wai don miji ya so matarsa, ko mace ta so mijinta (kamar “maliki yaumiddin” sai a fadada mimum a sanya sunan matar a sama, na mijin a kasa). To wannan dai shirka ne.
An samu Hadisi daga Abdullahi dan Ukaimu daga Annabi (S.A.W) yana cewa, “Duk wanda ya rataya wani abu (laya ko guru ko kambu ko daga ko wuri da sauransu) to za a rataya imaninsa ga wannan abin.” (Ahmad da Tirmizi suka ruwaito). Ahmad kuma ya ruwaito wani Hadisin amma daga Rufa’i ya ce masa, “Ya Rufa’i, kila ka yi tsawon kwana. To idan har Allah Ya sa ka yi tsawon kwana, ka bai wa mutane labari cewa wanda ya kulle gemunsa ko ya rataya laya ko ya yi tsarki da kashin dabba ko da kashi, to Annabi Muhammadu (S.A.W) ba ruwansa da shi”.
An samu wani Hadisi daga Sa’idu dan Jubair, ya ce wanda ya tsinke wata laya daga wani mutum to za a ba shi ladan wanda ya ‘yanta kuyanga (Waki’u ne ya ruwaito). Kuma an samu wani Hadisi daga Ibrahim ya ce su Sahabbai sun kasance suna kin laya dukkanta, wacce aka yi ta da ayoyin Al-kur’ani da kuma wacce ba Alkur’ani ba (Saboda shirka ne).
Babi na Tara
Neman albarka da itaciya ko dutse ko makamantansu Allah Ya ce, “Ku ba ni labari, shin Lata da Uzza da Manata na ukunsu (suna iya amfanarwa ko su cutar?)” (An’Najmi, 19).
An samu Hadisi daga AbiWakil Al-laithiyyi ya ce, mun fita da Annabi (S.A.W) zuwa yakin Hunain lokacin muna sababbin musulunta. Su mushirikai suna da wata itaciyar magarya wacce suke rataya takubbansu a kanta. Saboda yawan rataya a kanta suna kiranta “Ma’abuciyyar rataya”. Sai muka zo za mu wuce wata magarya sai muka ce, “Ya manzon Allah, ka sanya mana magarya mana da za mu rika rataya takubbammu kamar yadda su ma suke da magarya’. Sai Annabi (S. A.W) ya yi kabbara ya ce. “Kun bi hanyar da Yahudawa suka bi. Kuma na rantse da wanda rai na yake a hannunSa, kun fadi daidai da abin da bani Isra’ila suka cewa Annabi Musa (A.S.), “ka sanya mana abin bauta kamar yadda mutanen Fir’auna suke da abin bauta”. Sai Musa (A.S) ya fada wa mutanensa, “ku mutane ne jahilai”. Sai Annabi (S.A.W) ya ce, “kuma dai za ku bi hanyar wadanda suka gabace ku.” (Watau Yahudu da Nasara).
Babi na Goma
Yanka don wanin Allah:
Allah Yana cewa a cikin Alkur-ani, “ka ce (Ya Muhammad), sallah ta da yanka ko sukar abin hadaya da rayuwa ta da mutuwa ta na Allah ne Ubangijin talikai. Ba shi da abokin tarayya. Da haka aka umurce ni, ni ne farkon mai mika wuya.” (Anam-163). Allah kuma Yana cewa, “ka yi sallah don gode wa Ubangijinka, kuma ka yi yanka don neman yardar sa.” (Al-kauthar, 2).
An samu Hadisi daga Aliyu (R.A) yace, Annabi (S.A.W) ya zanta min kalmomi hudu inda ya ce, “Allah Ya tsine wa wanda ya yi yanka don wanin Allah; Allah Ya tsine wa wanda ya zagi mahaifansa; Allah Ya tsine wa wanda ya kirkiro bidi’a; Allah Ya tsine wa wanda ya kara iyakar kasa”. 6 (Bukhari da Muslim suka ruwaito).
An samo Hadisi daga Darik dan Shihab ya ce Annabi (S.A.W) ya bada labarin wadansu mutane biyu, daya daga cikinsu ya shiga aljanna saboda dalilin kuda, daya kuma ya shiga wuta saboda dalilin kuda. Sai Sahabbai suka ce, yaya za a yi mutum ya shiga aljanna saboda kuda wani kuma ya shiga wuta saboda kuda? Sai Annabi ya ce, “Wadansu mutane ne da gunkinsu suka tsare hanya. Duk wanda zai wuce sai ya gabatarwa gunkinnan wani abu. Sai wadansu mutane biyu suka taho. Sai suka ce wa daya daga cikin mutanen nan biyu, ‘ka bada wani abu ga gunkin nan’. Sai ya ce musu, ‘ai ba ni da wani abu da zan bai wa gunkin. Sai suka ce, “ai ko kuda kana iya kashewa ka bayar! Sai ya ce, ‘kuda kawai?! Suka ce ‘e.’ Sai ya kashe kuda ya sanya a gaban gunkin. Sai suka bar shi ya tafi. dayan kuma sai suka ce masa, ‘ka gabatarwa gunkin da wani abu mana’. Sai ya ce musu, ‘ai na yi alkawari ba zan yi wani abu ba, babba ko karami domin wanin Allah’. Sai suka kashe shi. Sai Annabi ya ce, “na farkon da ya kashe kuda ya gabatarwa gunki dan wuta ne, na biyun da ya ki gabatar da kudan dan Aljannah ne.” 7 (Ahmad ne ya ruwaito).