✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tattalin arzikin Najeriya ya kama hanyar rugujewa – Sanusi

Sarkin ya alakanta hakan da ci gaba da karyewar darajar danyen mai.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kuma tsohon Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya yi gargadin cewa tattalin arzikin Najeriya ya kama hanyar rugujewa sakamakon karyewar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Sarkin, wanda ke wadannan kalaman a Kaduna yayin taron zuba jari na Jihar karo na shida (KadInvest6.0) ranar Juma’a, ya kuma ce baya ga kalubalen da kasar ke fuskanta wajen hako man, darajarsa na ci gaba da faduwa ne sakamakon alkadarin injina masu amfani da shi na dada karyewa a duniya.

Ya ce makomar kasashe yanzu ta ta’allaka ne a kan ilimi mai alaka da tattalin arziki, wanda kuma shi ne taken taron na bana.

Sai dai tsohon Gwamnan na CBN ya koka kan cewa Najeriya na bayan kasashen Afirka da dama ta bangaren kirkira, inda take a matsayi na 114 a jerin kasashe masu kirkira na duniya.

Sanusi ya ba da misali da kasar Ghana, wacce ya ce duk da irin kankantar tattalin arzikinta, ta ware kudade sosai ga bangaren ilimi, inda ya koka kan cewa Najeriya kuwa kaso bakwai cikin 100 kawai ta ware wa bangaren.

Ya ce, “Takwas daga cikin ’yan Najeriyan da suka fara Firamare ne kawai ke iya kammala karatunsu har matakin jami’a.

“A duniya yanzu haka, alkiblar aiki ta sauya. Kaso 30 zuwa 40 cikin 100 na ma’aikata a kasashen da suka ci gaba na bukatar karin ilimi nan da 2030. Kuma menene manyan abubuwan da za su tafiyar da wannan makomar?… Ilimin Fasahar Sadarwa (ICT) ne da yin aiki daga gida kamar yadda muka gani yayin annobar COVID-19.

“Ana samun karuwar fasahar zamani. Nan ba da jimawa ba, injinan mutum-mutumi za su maye gurbin mutane a kasashe da dama, ta yadda zai kasance masu aikin yi a wajen sune kawai masu kula da injinan da masu kera su ko kuma masu gyara su.

A wani labarin kuma, Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce za ta bullo da ilimin Fasahar Sadarwa (ICT) a makarantun koyar da sana’o’i da makarantun Firamare da na Sakandire da ke fadin Jihar.

Gwamnan Jihar, Nasir El-Rufa’i ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai a taron, inda ya ce gwamnatinsa ta fuskanci cewa makomar duniya ta ta’allaka ne ga fasahar sadarwa.