✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tattalin arzikin Jamus ya shiga mawuyacin hali

Kayayyakin masarufi sun tashin gwauron zabi a kasar.

A farkon 2023 ne tattalin arzikin Kasar Jamus ya shiga mummunan yanayi na durkushewa, inda iyalai suke gwagwarmaya da tashin farashi na kayan masarufi.

Kayayyakin da ake samarwa a kasar sun ragu da kashi 0.3 a watannin farko na shekara nan, a lokacin da aka yi gyaran farashi, kamar yadda hasashe na biyu daga ofishin kididdigar kasar ya bayyana a ranar Alhamis.

Wannan ya faru ne sakamakon karyewar tattalin arzikin da aka samu ta kashi 0.5 a wata uku na karshen 2022.

Karo na biyu ke nan a jere da kasar ta bayyana durkushewar tattalin arzikinta.

Alkaluman yawan kayan da Jamus ke samarwa a cikin gida na nuna “Alamu marasa kyau”, in ji Ministan Kudi, Christian Lindner a ranar Alhamis.

Ya kara da cewa idan aka kwatanta Jamus da sauran kasashe da suka ci gaba, to za a ga tattalin arzikinta na durkushewa.

Ya ce “Ba na son Jamus ta yi sakaci da zai janyo mu kaskanta zuwa matakin karshe.”

Ministan na nufin kawo hasashen da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya yi kan shiga matsin tattalin arziki a Jamus da Birtaniya da wasu kasashen Turai.

“Mmasu sayen kayayyaki a Jamus suna ta kokawa da tattalin arzikin da ke faduwa”, in ji Andreas Scheuerle, mai nazari da bincike a DekaBank.

Sayen kayayyaki da iyalai ke yi ya ragu da kashi 1.2 bayan hawa da saukar farashi da kuma gyaran lokaci da aka yi.

Kazalika kudaden da gwamnati ke kashewa sun ragu da kashi 4.9.

“Yanayin dumama gari a lokacin sanyi, sake dawowar hada-hadar masana’antu, tare da taimakon sake bude China, da kuma saukin isar da kayayyaki ga jama’a, su kadai ba su isa mu fita daga matsin tattalin arziki ba”, in ji shugaban ING Carsten Brzeski.

Wani abu da ya sha bam-bam da wannan kuma shi ne yadda zuba jari ya karu a watanni uku na farkon wannan shekarar, bayan raunin da aka samu a watanni shida na karshen 2022.

“Farashin makamashi ya yi tashin gwauron zabi har zuwa tsakiyar sanyi”, in ji shugaban tattalin arziki na bankin Commerzbank.

Ba za a iya rabuwa da barazanar durkushewar tattalin arziki ba, kuma a yanzu tambayar ita ce ko za a samu ikon farfadowa a watanni shida na karshen shekara.

Brzeski na ING ya kara da cewa “Duba zuwa ga sama da watanni uku na farko, fatan da ake da shi a farkon shekara ya kau sakamakon wannan yanayi da ake fuskanta.”