✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tasirin kaunar juna a tsakanin mutane —Hadiza Gabon

Jaruma a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Hadiza Aliyu wadda aka fi sani da Hadiza Gabon, ta bayyana muradin da take da shi na ganin…

Jaruma a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Hadiza Aliyu wadda aka fi sani da Hadiza Gabon, ta bayyana muradin da take da shi na ganin mutane suna nuna kauna a tsakaninsu. 

Fitacciyar jarumar ta bayyana wa Aminiya cewa babban abun da yake faranta mata ya kuma kawar mata dukkan damuwa da radadi a ranta, shi ne ganin ta sanya farin ciki a zukatan mutane mabukata da masu rauni.

“Ya za ka ji a ranka idan ka ga mutane suna cikin walwala da nishadi saboda taimakonsu da ka yi.”

“Sai dai akwai mawadata kuma sun fi karfin komai amma su shantake ba sa iya taimakon mutanen da suke kwana da yunwa babu komai a cikinsu saboda tsabar rashin da suka tsinci kansu a ciki.”

“Abu ne mai dadi kwarai da gaske ka yi wa mutum abu komai kankantarsa da zai sanya masa farin ciki ko ka zama silar da za ta sauya masa rayuwa ya zama nagari da za a rika tunawa da shi.”

“Koyaushe mu yi iya bakin kokarinmu wurin taimakon mabukata da masu raunin cikinmu,” in ji Gabon.

A shekarar 2016 ne Hadiza Gabon ta kafa wata gidauniyar taimakawa mabukata wadda ake mata lakabi da “HAG Foundation”.

Aminiya ta fahimci cewa manufar gidauniyar ita ce; taimakon talakawa da masu rauni da mabukata ta hanyar ba su ilimi da kula da lafiyarsu da kuma wadata su da abinci.

Ita ce jarumar fina-finan Hausa ta farko a tarihin masana’antar Kannywood da ta fara taimaka wa mabukata ta wannan tsarin na kafa gidauniya.

“Ina kira ga jama’a da su dabi’antu da kyawawan halaye da kaunar juna da karfafa wa juna gwiwa don ta haka ne za a magance matsalolin kyama da tsangwama a tsakanin al’umma.

“Mutane suna jin dadin zamantakewarsu madamar soyayya da kaunar juna da taimakon juna ya zama jiki,” a cewar jarumar.