Tun a shekarar 2016, farashin man fetur yake ta hauhawa inda hakan yake ta sanya ’yan Najeriya cikin wani mawuyacin hali, saboda yadda farashin yake karuwa ba tare da sauka ba.
A watan Mayun shekarar 2016, farashin man fetur ya karu zuwa Naira 145 kan kowace lita daga Naira 86.50 da kasar ta gada daga mulkin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.
- An kara farashin man fetur zuwa N151.56 a Najeriya
- An kara farashin wutar lantarki a Najeriya
- Farashin man fetur ya koma N138.62 ga dillalai —NNPC
A watan Maris na 2020, farashin litar man fetur ya sauka zuwa Naira 125 daga Naira 145.
A watan Mayu na 2020, Hukumar Kayyade Farashin Man Fetur (PPPRA) ta sanar da karin farashin daga Naira 121.50 zuwa Naira 123.50 kan kowace lita.
Amma a watan Yuli 2020, sai farashin ya karu daga Naira 140.80 zuwa Naira 143.80.
A watan Agusta 2020, an sake samun sauyin farashin tsakanin Naira 145.86 da Naira 148.86.
A yanzu haka sauyin farashin da aka samu shi ne wanda ya karu a ranar Laraba 2 ga Satumba 2020, inda aka samu karin farashin zuwa Naira 151.56.
Yayin da ’yan kasuwa kuma suka ce za su kara nasu farashin sama da Naira 151.56.