✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tashin Dala: Akwai yiwuwar farashin mai ya tashi

Da zarar Dala ta tashi, farashin kayayyaki kan tashi

An wayi gari farashin Dalar Amurka ya tashi zuwa Naira 925 kamar wadda wakilinmu ya gano a kasuwar canji a Najeriya inda ta kusa kaiwa Naira 1,000.

Idan ba a manta ba, Shugaban Kasa Bola Tinubu a ranar rantsar da shi ya bayyana cewa zai kawo sauye-sauye a bangaren harkokin kudade na Najeriya, inda daga ciki ya bayyana daidaita farashin Dala, ta yadda yanayin kasuwa ne zai rika alkalanci.

Ke nan ’yan kasuwa da bankuna suna da damar ayyana farashin Dalar idan suna da ita, maimakon da, wanda Babban Bankin Najeriya (CBN) ne kadai ke iya ayyana farashin na gwamnati, wanda ke da alaka kai-tsaye da farashin yadda yake a bankuna.

Sai dai sanannen abu ne a Najeriya cewa farashin Dala yana da alaka da farashin kayayykin masarufi da sauran abubuwan bukata.

Da zarar Dala ta tashi, farashin kayayyaki kan tashi, inda ya zama sanannen magana wajen ’yan kasuwa, za ka ji suna cewa, ‘ka san Dala ta tashi.’

Daga cikin abubuwan da farashin Dala yake shafa, akwai man fetur, wanda har yanzu Najeriya shigo da shi take yi.

A watan jiya wato Yuli, Aminiya ta ruwaito cewa farashin man fetur ya kai Naira 615, wanda lamarin ya tayar da hazo a kasar.

Sai dai ganin yadda dalar take kara hauhawa, akwai yiwuwar farashin man zai iya karuwa.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, Aminiya ta lura gidajen mai ba su kara kudin man ba.