✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin sojin Nijar ta nada ministoci

Nada majalisar ministocin na zuwa ne a ranar da kungiyar ECOWAS za ta yi taro bayan wa'adin da ta sake ba wa masu juyin mulkin…

Shugaban gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ya nada ministoci 21, karkashin jagorancin sabon Fira Ministan kasar.

Shugaban mulkin sojin, Janar Abdoulrahamane Tchiani ya sanar da mambabin majalisar ministocin ne a ranar da kungiyar ECOWAS za ta fara taron da za ta cim-ma matsaya kan sabon matakin da za ta dauka kan juyin mulkin Nijar din.

Abin da Sanusi II ya tattauna da gwamnatin sojin Nijar

Fira Minista Ali Mahaman Lamine Zeine da sojojin suka nada ne zai jagoranci ministocin, wadanda daga cikinsu sojoji za su jagoranci ma’aikatu shida — tsaro, harkokin cikin gida, lafiya, sufuri, muhalli da kuma matasa da wasanni .

Ga jerin sunayen ministocin:

  1. Fira minista kuma Ministan Kuɗi da Tattalin arziki — Lamine Zeine Ali Mahamane
  2. Karamin Ministan Tsaron ƙasa — Laftanar-Janar Salifou Mody
  3. Karamin ministan harkokin cikin gida da tsaron al’umma — Birgediya-Janar Mohamed Toumba
  4. Ministan Matasa da Wasanni — Kanar-Manjo Abdourahamane Amadou
  5. Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a — Kanar-Manjo Garba Hakimi
  6. Ministan sufuri — Kanar Salissou Mahaman Salissou
  7. Ministan Muhalli da Tsafta — Kanar Maizama Abdoulaye
  8. Ministar Ilimi da Koyar da Sana’oin Hannu da Bunƙasa Harsunan ƙasa — Elizabeth Cherif
  9. Ministar Kwadago da Samar da Ayyukan — Aissatou Abdoulaye Tondi
  10. Ministan Jin Kai da Agajin Gaggawa — Aissa Lawan Wandarama.
  11. Ministan Harkokin Waje da Haɗa kan ’Yan Nijar Mazauna Ketare — Bakary Yaou Sangare
  12. Ministan Kula da Majalisar ƙasa da Tabbatar da Lafiyar Cikin Gida — Soumana Boubacar
  13. Ministan Noma da Kiwo — Mahaman Elhadj Ousmane
  14. Ministan Ilimi Mai Zurfi da Binciken Kimiyya da Fasaha — Farfesa Mahamadou Saidou
  15. Ministan Shari’a da Kare ’Yancin Dan-Adam — Alio Daouda
  16. Ministan Tsare-tsaren da Samar da Gidaje — Salissou Sahirou Adamou
  17. Ministan Man Fetur da Ma’adinai da Makamashi — Mahaman Moustapha Barke
  18. Ministan Yawon Buɗe Ido da Sana’oi — Guichen Agaichata Atta
  19. Ministan Sadarwa da Bunƙasa Fasahar Zamani — Sidi Mohamed Raliou
  20. Ministan Kasuwanci da Masana’antu — Seydou Asman
  21. Ministan Harkokin Kuɗi a Ofishin Firaminista — Moumouni Boubacar Saidou

Hakan kuwa na zuwa ne washegarin da Janar Tchiani ya karbi bakuncin Khalifan Darikar Tijjaniyya na yakin Yammacin Afirka, Malam Muhammadu Sanusi II a birnin Yamai, bayan gwamnatin sojin ta ki amincewa da ziyarar wakilan ECOWAS da kasashen duniya domin sulhu.

A farkon makon nan ne sojojin suka nada tsohon ministan kudin kasar, Ali Mahaman Lamine Zeine a matsayin fira minista, kimanin mako uku bayan sun kifar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum, da har yanzu suke tsare da shi.