Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi kirag ga ’yan kasuwa da kada su kara farashin kayan masarufi kudi domin bai wa talakawa damar yin azumin watan Ramadan cikin kwanciyar hankali.
Sarkin ya kuma bukaci masu hannu da shuni da su taimaka wa mabukata a lokacin azumin da ke tafe domin rage masu radadin matsin rayuwa da ake ciki.
Ya kuma yi fatan Allah Ya ba mu ikon ganin watan na Ramadan cikin koshin lafiya, kuma Ya amsa mana ibadunmu da addu’o’in da za mu yi a cikin watan.
- Daurawa Ya Ba Bata Gari Wa’adin Sati 2 su tuba
- Yadda Jama’a Ke Shan Wahalar Haɗa Lambar NIN da BVN a Bankuna
Basaraken ya yi kiran ne a Zariya lokacin kaddamar da wani littafi mai suna ‘Dauloli A Kasar Hausa’ wanda Farfesa Sa’idu Mohammed Gusau ya wallafa.
A ranar Litinin ko talata na mako mai zuwa ne ake sa ran al’ummar Musulmi za su fara azumin watan Ramadan na wannan shekarar.
Da yake yaba wa mawallafin littafin, Sarkin Kano ya bayyana cewa littafin ya yi bayani dalla-dalla game da masarautun kasar Hausa kamar Kano da Katsina da Zamfara da Kebbi da kuma Zazzau.
Ya kara da cewa littafin ya yi cikakken bayani game da tsarin yadda ake gudanar da mulki a wadannan dauloli da tsarin kasuwanci da al’adu da kuma dabi’unsu.
Wanda ya yi nazari a kan littafin, Farfesa Ahmed Zariya na Jami’ar Jihar Kaduna, ya ce littafin mai shafuka 356 ya yi bayani ne a kan tarihi da mulki da siyasa, dabi’u da al’adun daulolin Hausa tun daga lokacin kafuwarsu zuwa yanzu.
Ya kara da cewa yana da muhimmanci dalibai da masu gudanar da bincike a kan tarihi da harsuna su mallaki littafin.
A don haka sai malamin jami’ar ya shawarci malaman jami’a da kada su yi kasa a gwiwa yayin gudanar da aiyukan bincike.
Sanann ya bayyana takaicin sa bisa yadda wasu malaman jami’a ke yin watsi da harkokin bincike da zarar sun sami mukamin farfesa.
Mawallafin littafin, Farfesa Sa’idu Mohammed Gusau, ya ce an wallafa littafin ne da nufin samar da daidaito a rubutaccen tarihin daulolin Hausa, yana mai nuni da cewa yawancin binciken da aka gudanar a jami’o’i an yi su ne a kan tsirarun dauloli maimakon duka.
Ya kara da cewa an wallafa littafin ne domin karfafa dankon zumunci da hadin kai a tsakanin daulolin kasar Hausa da sauran ’yan Najeriya.