’Yan sandan Turkiyya sun kama akalla mutum 46 bisa zargin su da hannu a fashewar wani abu a tsakiyar birnin Istanbul.
Bam din ya tashi ne a kan wata gadar masu tafiya a kasa da ke kan wani titin da mutane da yawa ke hada-hada a babban birnin kasar, a inda ya hallaka akalla mutum takwas.
- Bam ya hallaka mutum 4, ya jikkata wasu 38 a Turkiyya
- Mutum 16 sun mutu, 21 sun jikkata a hatsarin mota a Turkiyya
A hirarsa da ‘yan jarida, Ministan Harkokin Cikin Gida na kasar, Suleyman Soylu, ya ce a ciki har da wadanda ake zargi da tayar da bam din.
Ministan ya dora alhakin tayar da bam din akan haramtacciyar Kungiyar Gwawarmaya ta Kurdawa (PKK), yana mai cewa, suna da yakinin umarnin tayar da bam din ya fito ne da Ain Al Arab (Kobane) da ke arewacin Syria.
“Za mu mayar da maratani kan wadanda ke da alhakkin kai wannan mummunan hari ta’addanci” in ji Ministan.
Shugaban kasa Recep Tayib Erdogan ya bayyana tashin bam din da cewa, bakin zalunci ne mai dauke da kamshin ta’addanci.
Ministan Shari’ar kasar Bekir Bozdag ya fada wa wani gidan talbijin cewa, suna zargi wata mace da ta zauna sama da kimannin mintuna 40 a wani wurin hutawa a titin Istiklal ce ta tayar da Bam din.
Domin barin ta wurin ke nan, bam din ya tashi, a cewarsa