✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan karfafa dangantakar diflomasiyya da sauran kasashen duniya —Erdogan

Shugabannin kasashen duniya akalla 21, da firaminista 13 ne suka halarci rantsar da Erdogan a birnin Ankara.

An sake rantsar da shugaban Recep Tayyip Erdogan a matsayin shugaban kasar Turkiya a karo na uku, bayan da ya lashe zaben zagaye na biyu karo na farko da aka taba gudanarwa a kasar.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sha alwashin karfafa dangantakar diflomasiyya da sauran kasashen duniya a yayin da ya dauki alkawarin inganta tattalin arzikin Turkiyya.

Haka kuma, Shugaba Erdogan ya dauki alkwarin samar da sabbin sauye-sauyen da za su ciyar da kasar gaba.

Erdogan ya fadi hakan ne bayan shan rantsuwar shugabancin kasar a sabon wa’adin mulki a karo na uku a ranar Asabar, a sakamakon nasarar da ya samu a zagaye na biyu na zaben kasar da ya gudana a makon da ya gabata.

Shugaban ya samu nasarar lashe zaben zagaye na biyu da aka gudanar a ranar 28 ga watan da ya gabata, duk kuwa da hadakar da jam’iyun adawar kasar suka yi, ga matsalar tattalin arziki da kuma ta ibtila’in girgizar kasar da aka samu a watan Fabarairu da ya yi sanadiyar mutuwar mutane samada dubu 50.

Erdogan ya samu kashi 52.18 na kuri’un da aka kada, ya yin da babban abokin hamayyar sa Kemal Kilicdaroglu ya samu kashi 47.82.

Shugaban mai shekaru 69 da ya kwashe sama da shekaru 20 yana mulkin kasar, a yanzu zai sake jagorantar ta na tsawon shekaru 5, kuma nan gaba kadan ake saran ya sanar da ‘yan majalisar zartarwarsa wadanda za su tunkari kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

Wannan ne karo na biyar da Erdogan ke jagorantar kasar, domin kafin zamowa shugaban kasa, ya taba yin faraminista karo biyu tsawon shekaru 10, sannan ya zamo shugaban kasa na tsawon shekaru 10, yanzu kuma ya dora a kan hakan.

Shugabannin kasashen duniya akalla 21, da firaminista 13 ne suka halarci bikin shan rantsuwar na Erdogan a birnin Ankara.