✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karya ta kai kwikwiyonta mara lafiya asibiti

Idan ba don gajeran bidiyon da kyamarorin na’urar CCTV suka ɗauka ba, da alama yawancin mutane za su yi tunanin wannan labarin ba zai iya…

A kwanakin nan ne wani asibitin kula da dabbobi a kasar Turkiyya ya wallafa wani labari mai ratsa jiki na wata karya da ba ta da masauki ta ɗauki ɗanta da ya suma a bakinta ta ajiye shi a kofar asibitin kamar mai neman taimako.

Idan ba don gajeran bidiyon da kyamarorin na’urar CCTV suka ɗauka ba, da alama yawancin mutane za su yi tunanin wannan labarin ba zai iya zama gaskiya ba.

Wani asibitin dabbobi a Unguwar Adnan Kahveci da ke Beylikduzu, a lardin Istanbul na ƙasar Turkiyya, kwanan ya fitar da rahoton ɗaya daga cikin muhimman harkokin asibitin.

A ranar 13 ga watan Janairu, wani masoyin dabbobi ya kawo wani matashin kwikwiyo da suka same shi a kan titi, yana mai cewa shi kaɗai ne ya tsira daga cikin sauran ’yan uwansa.

Jami’an asibitin sun ruga don yi wa ɗan kwikwiyon magani sai ga wata karya ta fito daga bakin ƙofa da wani kwikwiyo a sume a bakinta.

Wani masani ne ya lura da wannan dabbar da ta ƙaurace masa, sai ya garzaya domin ya kula da ’ya’yanta, waɗanda ke fama da rashin lafiya kuma jikinta ya yi rauni sosai.

Kyamarorin sa-ido daga cikin asibitin sun nuna mahaifiyar kwikwiyon da ke cikin damuwa tana bin likitocin dabbobi zuwa asibitin kuma ta zuba musu ido, yayin da suke kula da jaririnta da ya suna.

An yi sa’a, Dakta Baturalp Oghan da tawagarsa sun sami damar ceton ɗan kwikwiyon kuma yanzu dukan karnukan suna murmurewa a asibitin.

“Komai na tafiya yadda ya kamata. Maganin da ake yi wa kwikwiyon da dan’uwansa zai ci gaba na ɗan lokaci kaɗan.

“A wannan lokacin, ba ma karɓar bakin marasa lafiya saboda kula da lafiyarsu,” in ji Dokta Oghan.

“Mahaifiyar karyar tana samun sauƙi sosai. Labarinta ya birge mutane da yawa, karyar tana da basira da kulawa.

“Tana nuna irin soyayyar da uwa karya take yi wa ’ya’yanta.”

A bayyane yake, nonon mahaifiyar ba ya isa ta ci gaba da shayar da sauran ’ya’yanta gaba ɗaya, wanda shi ne dalilin da ya sa wasu ’yan kwikwiyon suka mutu cikin rashin shayarwar, don haka asibitin yana kara kula da ’yan kwikwiyon da suka tsira da ransu da taimakon ciyar da su.