Wani abin takaici ya sake afkuwa a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa a Jihar Borno mai cike da tashin hankali, yayin da wani bam ya tarwatse a safiyar Asabar da rana, inda aƙalla mutane takwas ne suka mutu.
Wasu shaidun gani da ido na nuni da cewa fashewar bam ɗin da ake kyautata zaton mayaƙan Boko ne suka dasa shi ya tarwatsa wata motar bas ƙirar Toyota “Hummer Bus” da ke ɗauke da fasinjoji zuwa Maiduguri babban birnin Jihar Borno.
Wata majiya mai tushe da aka zanta da ita, ta tabbatar da cewa aƙalla mutane bakwai da suka haɗa da direban motar ne ake fargabar sun mutu a wannan mummunan fashewar.
Titin Maiduguri zuwa Damboa ya kasance muhimmiyar hanyar mota da ta haɗa birnin Maiduguri zuwa ƙaramar hukumar Damboa da sauran al’ummomin kudancin Borno wadda a kullum ake fargabar bin ta lura da cewar tana gab da dajin Sambisa.
Don haka wannan lamari na baya-bayan nan ya zama babban abin tunatarwa game da barazanar tsaro da ke fuskantar matafiya da ke bin wannan hanya mai muhimmanci.
Har yanzu dai hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba, har ya zuwa lokacin kammala wannan rahoto.
To sai dai kuma babu shakka wannan harin zai ƙara dagula al’amura game da lafiyar masu tafiye-tafiye da sufuri a yankin da kuma yankin da ake da ’yan tada ƙayar baya a yankin Arewa maso Gabas.
Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya kai ziyarar jajantawa ga waɗanda wannan haɗari ya rutsa da su da ke karɓar magani a babban asibitin ƙwararru na Maiduguri, inda gwamnan ya bada umarni da a yi musu magani kyauta tare bai wa kowanne ɗaya daga cikinsu kyautar Naira dubu 50.