Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa kasarsa ta ja layi tsakaninta da Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu inda ta ce ba mutum ba ne da za ta iya magana da shi.
Turkiyya a wannan Asabar ta yi wa jakadanta da ke birnin Tel Aviv kiranye kan cewa ya koma Ankara domin tattaunawa a daidai lokacin da Falasdinawa ke ci gaba da kai hare-hare kan Gaza.
- BUA da Dangote na zargin yi wa juna zagon kasa a harkokin kasuwanci
- Sojoji sun kai hari kusa da fadar Shugaban Kasar Guinea
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Turkiyya ta ce an yi wa Sakir Ozkan Torunlar kiranye ne “sakamakon irin bala’in da ke faruwa a Gaza,” a sanarwar da ta fitar ranar Asabar.
Sakamakon “irin hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa kan farar hula, da kuma kin amincewar da Isra’ila ta yi na tsagaita wuta, da kuma ci gaba da kawo cikas ga ayyukan shigar da kayan agaji, an yanke shawarar yi wa jakadanmu da ke Tel Aviv kiranye,” a cewar ma’aikatar.
Tun da farko a ranar Asabar, Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa kasarsa ta ja layi tsakaninta da Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu haka kuma za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin ta kai take hakkin bil adama da kuma laifukan yakin da Isra’ila ta yi a gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya.
Firaiministan “ba wani ne da za mu ci gaba da magana da shi ba, mun ja layi tsakaninmu da shi,” kamar yadda Erdogan ya shaida wa manema labarai a cikin jirgin shugaban kasa a hanyar komawa daga Kazakhstan bayan ya halarci Taron Kasashen Turkawa.
Ya bayyana cewa Netenyahu ya rasa goyon bayan ‘yan kasar Isra’ila haka kuma yana neman goyon bayan kisan kiyashi ta hanyar maganganun addini.