“Ba mu zo nan ba don mu shigo da wani abu ba ta barauniyar hanya akan bukatar wata shiyya. Don haka wannan taron bai kamata ya zama yana da wata boyayyiyar manufa ba. Idan har akwai wani batu da ake so a gabatar, to, a gabatar da shi ta yadda za mu tunkare shi.” Wadannan kalamai na daga cikin kalaman da Alhaji Ishak Modibbo Kawu, Wakilin taron kasa daga kungiyar manyan Editoci ta kasa baki daya, ya furta a cikin makon jiya a lokacin da ta bayyana wasu Wakilan taron na kokarin cusa wani Kundi mai shafuffuka 102, (da suke begen ganin daga karshe ya zama rahoton da taron zai amince da shi, kuma ya zama sabon kundin tsarin mulkin kasar nan). Duk kuwa da sabon kundin bai kunshi akasarin batutuwan da rahotannin Kwamitocin taron 20, suka tattauna ba, amma kuma ake kokarin cusa shi cikin rahoton karshe na taron kasar, ma`ana a neman shege ya fi mai uba.
A ranar Lahadi 29-06-14, `ya`yar wannan jarida Sunday Trust, ta dauko wani labari, inda ta ka tako zargin wasu Wakilin taron suna kokarin cusa wancan kundi, da aka yi wa lakabin Taron kasa 2014, Yarjejeniyar Shiyyoyi shidda na kasar nan.”Wasu daga cikin batutuwan da wancan haramtaccen kundin ya kunsa sun hada da mayar da kashi 13, cikin 100, da ake ba jihohi masu arzikin man fetur daga kudin albarkatun man fetur da ake hakowa a jihohinsu zuwa kashi 50, cikin 100. kara kirkiro sababbin jihohi 19, uku daga kowace shiyya, in ban da shiyyar Kudu maso gabas da za ta samu hudu, sabbin jihohin da kundin ya riga ya ambata sunayensu da kuma daga cikin jihohin da za kirkiro su.
Sauran manyan batutuwan da wancan kundi ya kunsa, sun hada da babbar Ajandar Wakilan taron kasar da suka fito daga shiyoyin Kudu maso kudu da na Kudu maso yamma da na Kudu maso gabas da wasu da suka fito daga wasu sassan shiyyar Arewa ta tsakiya, sun hada da daina raba arzikin kasar nan da Majalisun kananan Hukumomin kasar nan 774, da nufin ke nan an soke tsarin kananan Hukumomi (kodayake Wakilan taron irin su Farfesa Jerry Gana, sun ce ba a suke kananan Hukumomin ba) da kuma tabbatar da tsarin mulkin karba-karba tsakanin kudu da Arewa, akan mukamin shugaban kasa da kuma tsakanin mazabun `yan Majalisar Dattawa a jihohi, akan mukamin gwamnonin jihohi, a zaman kuma mulkin shekaru shidda zaman falle daya, da batun kirkiro `Yan sanda jihohi da kuma samar wa kowace shiyya tsarin mulkin kanta. Jaridar ta yi zargin cewa ana kokarin ganin an shawo kan Wakilai da ake ganin za su iya daga kara ta hanyar ba su makudan kudi.
Bayan bayyanar wannan rahoto da irin matsin lambar da aka rika samu daga musamman Wakilan taron da suka fito daga jihohin Arewa, Mataimakin Shugaban taron, Farfesa Bolaji Akinyemi da shi kansa wanda ake zargin shi ne babban dillalin tallata sabon Kundin Cif Raymond Dopkesi, duk sun magantu, da cewa sun san da zaman wancan Kundi, da ma irin kokarin da suke wajen ganin sun tallata shi, ta hanyar tuntubar Wakilan da suka ga za su iya tafiya da su, har kwalliiya ta biya kudin sabulu. Dukkan mutanen biyu sun tabbatar a zauren taron cewa wasu Wakilan Arewar da suka fi nuna adawa da sabon Kundin sun san da zamansa.
Farfesa Akinyemi, ya tabbatar da cewa lallai kam ya tuntubi shugaban Wakilan Arewa kuma tsohon Sufeto Janar na `yan Sanda Alhaji Ibrahin Coomassei, wanda har ya tura masa wani ayari da suka fara tattaunawa da su. Ya ce shi kuma ya yi haka ne bisa fahimtar da ya yi akan yadda tunda aka fara taron ya fahimci cewa a cikin Wakilan taron akwai masu ra`ayin a rubuta sabon tsarin mulki, akwai kuma masu ra`ayin a yi taro a bada sakamakon abin da duk taro ya cimmawa, don haka in ji shi akwai bukatar samun daidaituwar magana.
A takaicen-takaitawa mai karatu ta haka aka kafa wani Kwamiti da aka kira ”Kwamitin samun mafita don gina kasa,” Kwamitin da kowace shiyya ta bada Wakilai uku, aka tada Kwamitin mutane 18, inda daga karshe kamar yadda Cif Dopkesi ya fadi aka haifar da wancan sabon Kundi da akasarin batutuwan da taro bai tattauna su ba, kuma shi ake son ya zama sabon Kundin tsarin mulkin kasar nan.
Ya zuwa yanzu Farfesa Auwalu Hamisu Yadudu daya daga cikin Wakilan Arewa a wancan Kwamitin na Cif Dopkesi ya riga ya nisanta Arewa baki daya daga wancan sabon Kundi da abubuwan da ya kunsa, shi kan sa shugabancin Taron kasar ya nisanta kansa da wancan Kundi akan bai san da shi ba, amma kuma duk da haka sai ga shi a zaman taron na ranar Juma`ar da ta gabata shugabannin Arewan, sun nisanta kansu da ganin wasu kudurce-kudurce da suka samu kansu a cikin daftarin da suke shiryawa da zai zama rahotansu na karshe, kamar batun soke Majalisun kananan Hukumomi, da makamanta batutuwa da aka dauko daga wancan Kundi na su Cif Dopkesi.
Ba wani sabon abu ba ne a kasar nan a duk lokacin da za a shirya wani taro da zai fitowa da kasa makoma irin ta zamantake da rabon tattalin arzikin kasa da tsari siyasa da na tattalin arziki da sauran muhimman batutuwa, to, kuwa za ka taras Gwamnatin da ta kafa irin wannan Kwamiti takan yi kokarin ganin bukatunta sun kai labari. A irin haka yau shekaru sama da 15, ana mulkin dimokuradiyya, amma kullum ake cewa tsarin mulki ya gaza, bisa ga zargin sojoji suka shirya shi. Haka labarin yake a shekarar 2007, lokacin da Majalisun Dokoki na kasa suka yi aniyar gyaran Kundin tsarin mulkin kasar nan, sai da shugaban hadin gwiwar Kwamitin Sanata Ibrahim Mantu ya yi kokarin cusa tsarin tazarcen da shugaba Obasanjo ya cusa a cikin Kwamitinsa na taron makomar kasa da ya shirya a shekarar 2005.
Don haka irin abubuwan da suke gudana yanzu a taron kasar dama an saba da ji, da ganinsu, abin da kawai ya rage Wakilan Arewa, wadanda dama can tun farko da wannan nufakar aka sa suka zama marassa rinjaye da wakilai 192, ya yi da na kudanci suke 300, ya kamata su dage, su kara bude idanuwansu, don an ce aski in ya zo gaban goshi ya fi zafi. Ga sauran Wakilai kuma su sa ni cewa munafunci Dodo ne wanda ya kan ci mai shi. Allah na nan zai kuma yi mana maganin dukkan wani makiyin Arewa da mutanenta koda kuwa dan Arewan ne, kamar yadda ya yi akan shugabannin baya.
Taron kasa: Munafunci dodo yakan ci mai shi
“Ba mu zo nan ba don mu shigo da wani abu ba ta barauniyar hanya akan bukatar wata shiyya. Don haka wannan taron bai kamata…