Shugaban Hukumar Gudanarwar Hukumar NCC, Otunba Olabiyi Durojaiye, ya lissafa wasu daga muhimman nasarorin da hukumar da takwararta ta zartarwar hukumar suka samu a shekaru masu yawa yayin da ya bayyana niyyar hukumar ta tallafa wa shugabannin hukumar wajen bunkasa masana’antar tarho ta hanyar dora ta a kan hanyar doka da oda.
A jawabinsa na maraba a taron hukumar gudanarwar na bana, wanda ya gudana a otel din Bristol Palace da ke Kano, Snata Durojaiye ya bayar da takaitattun nasarorin da hukumar gudanarwar ta samu inda ya ce manufar taron wanda yake da jigon “Shugabanci da Aikin Nagari” an shirya shi ne don tattaunawa kan ayyukan bana da tsare-tsaren da aka yi don tunkarar badi, yadda za ta zama mai nasara. Ya ce an samu nasara a bana a karkashin jagorancin Farfesa Umar Dambatta, Babban Jami’i kuma Babban Kwamishina.
Durojaiye ya ce Hukumar NCC ta cimma burin bayar da gudunmawa ga tattalin arzikin kasa da ya kai na fiye da Naira tiriliyan 10 a zango kamar yadda hukumar ta yi taro da masu ruwa-da-tsaki da suka hada da hukumomin da sassan ma’aikatun gwamnati don tabbatar da hadin gwiwa da bunkasa ci gaba a vangaren tarho.
Dangane da bunkasa kayayyakin aiki, Durojaiye ya ce an samu fadadar sanya na’urorin samar da Intanet ta hanyar bayar da amincewa ga kamfanonin sanya na’urori masu lasisi a shiyyoyin kasar nan.
“Hukumar NCC ta karfafa ayyukan masana’antar sadarwa ta hanyar kokarin hukumar gudanarwa da kuma shirya taron wayar da kan masu ruwa-da-tsaki a shiyyoyin kasar nan,” inji Durojaiye
Dangane da batun bunkasa ayyuka da tafiyar da mulki, Shugaban Hukumar Gudanarwar NCC ya ce hukumar ta jagoranci mika kamfanin Etisalat saboda matsalar da kamfanin ya samu don tabbatar da ci gaba da kare ayyuka da karfafa masu zuba jari a masana’antar tarho.
Ya kara da cewa hukumar Gudanarwar NCC ta tallafa wa manufofin hukumar masu muhimmanci wajen ayyana shekarar 2017 a matsayin “Shekarar Abokan Huldar Tarho” daga bisani ta goyi bayan tsare-tsare daban-daban don kare sanarwa da karfafawa da ilimantar da abokan hulda. Durojaiye ya ce dukkan wadannan abubuwa za su ci gaba don samar da tasiri mai kyau a masana’antar.
Shugaban ya ce Hukumar Gudanarwar wacce kwanan nan aka sake karfafa ta da sababbin kwamishinoni biyar ta samu karfin da za ta tallafa da sanya shugabannin hukumar a kan doka don sauke nauyin da aka dora mata kamar yadda dokar da ta kafa hukumar ta shekarar 2003 ta tanada.
Daga bisani kwamishinonin hukumar gudanarwar hukumar sun ziyarci Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
Ayarin da Durojaiye ya jagoranta ya yaba da kishin kasa na Gwamnan wajen samar da ma’aikata a cibiyoyin sadarwa na gaggawa tare da yanayi don bunkasar tarho a jihar.
Da yake jawabi, Gwamna Ganduje ya bayyana godiyarsa ga Hukumar Gudanarwar NCC da ziyarar da suka kai masa. Ya yaba wa hukumar kan tabbatar da kamfanonin tarho sun samar da ingantaccen tarho ga mutanen Kano da Najeriya baki daya. Gwamnan ya yaba wa Hukumar NCC game da kokarin da take yi don ganin an fadada kimiyyar bayanai da sadarwa don bunkasa tsaron kasa.