Asalin Lere
Za a iya fassara Kalmar Lere a fulatanci da mazauni na dindindin. Asalin Lere wasu kabilu ne na Larabawan Sanhaja da suka zauna a wani yanki da ake kira Takrur a kasar Mauritania. Kakannin Lerewa sun fara yada zango ne a Futa Toro a kusa da Tekun Senegal tun a karni na 8, sannan kuma wasu bayanai suna nuna cewa akwai alaka ta auratayya tsakanin su da kabilun Fulanin Toronkawa da Larabawan Massufa a kudancin Sahara wadanda suka kirkiro tafiyar nan ta al-Murabitun a karni na 11. Daga Takrur sai suka yi kaura zuwa Kunta da Timbuktu.
A Timbuktu, sun taka rawar gani wajen tabbatar da Askia Muhammad a matsayin Sarkin Daular Songhay bayan faduwar mulkin Mali a karni na 15. Daga nan sai aka basu mulkin Gwamnan Timbuktu wanda ake kira da Timbuktu-koi. An samu gwamnoni a gidan da dama har aka kawo kan Umar bin Mahmud Akit wanda shi ne ya rasa mulkin ga Sa’dis na Moroko bayan mulkin Songhay ya fadi a hannun Moroko a shekarar 1591. Wasu daga cikin iyalan Akit da wasu ‘yan Fulani sai suka yi kaura daga Timbuktu a karni na 17 inda suka kafa garuruwa da dama, daga cikin su akwai guda biyu da suke amsa sunan Lere, daya a Kudu maso Yammacin Timbuktu dayan kuma yankin Dendi da ke kasar Burkina Faso a yanzu.
Daga yankin Nijar, sai suka ratsa ta Kudanci inda suka fado Arewacin Najeriya suka yada zango a yankin Zamfara a wani waje da ake kira Tsohon Banaga. A cikin shekarun 1750s wannan rukuni na Fulani wanda aka fi sani da suna Fulanin Wunti suka bar yankin Zamfara suka yi Kudu maso Yamma suka shigo Kasar Zazzau. Sun bar danu’wansu Mallam Muhammadu Dadi a Zamfara.
‘Yan uwan Muhammd Dadi, Muhammad Sambo da Muhammad Dabo (Titi) da Yunusa da sauransu wato Fulanin Wunti sai suka tafi ta Kudanci inda suka sauka a Zaria. Muhammad Sambo sai ya bar ‘yan uwanshi a Zaria ya tafi Kachia. Muhammad Dabo (Titi) shi ma sai ya bar danuwansa Yunusa a Jaji a kusa da Zaria inda ya tafi ta Kudu maso Gabashin Zaria zuwa wani waje kusa da inda garin dan Alhaji Gabas yake a yanzu ya yada zango. Muhammadu Dabo ana kiransa da ‘Titi’ ne sagoda saukaka sunan Fulani na‘Titiye’ wanda ke nufin ‘Makiyayi’.
A lokacin da suke zaune, sai wasu jama’a a karkashin Usman Biri wadanda suka gaji da zagaye-zagaye, suka fice daga ayarin, inda suka tafi Kudancin Bauchi, suka yaki kabilar Sayawa a kusa da Tafawa balewa suka gina zagayayyen gari da suka sa wa suna Leren-Zagezagi a shekarar 1790. Amma duk da haka mutanen Leren-Zagezagi suna kawo gaisuwa wajen Sarkin Habe na Zazzau, kuma haka aka ci gaba har sai lokacin da Mallam Yakubu ya yi yaki a shekarar 1806 inda ya samu nasarar hade su a karkashin sarautar Bauchi. Da ga nan ne aka mayar da sunan garin Leren-Bauchi.
Wannan ne yasa Muhammadu Dabo Titi ya rada wa masarautarsa suna Leren Zazzau a madadin ita Leren Bauchin bayan an tabbatar masa da sarautarsa a shekerar 1808.
Masarautar Lere
An kafa Masarautar Lere ne a shekarar 1808 a karkashin shugaban Fulanin Wunti Malam Muhammadu Dabo Titi. Wadannan Fulanin sun sauka a yankin Bauchi a karshen karni na 18 bayan sun baro Maru na Zamfara, inda suka fara yada zango a yankin Zaranda kafin jihadin Shehu dan Fodiyo.
Malam Muhammadu Dabo Titi ya matsa zuwa Toro inda ya gina gidansa a wani waje da ya sa wa suna Gyamzo, da haka ne aka sanya mutanen garin Wunti-Gyamzo.
Bayan Shehu Usmanu danfodi ya kaddamar da jihadi a 1804, sai Muhammadu Dabo Titi ya taimakawa Malam Yakubu wanda shi ne ya karbo tutan Bauchi. Sai Malam Yakubu ya nada Muhammadu Dabo Titi Sarkin Yaki, daga baya kuma ya bar wasurikinsa Fulata Barno mai suna Muhammadu Kusu sarautar. Dangin Muhammdu Kusu da Muhammadu Dabo Titi ne suke rike da sarautar Sarkin Yaki kuma Hakimin Lame tun wancan lokacin har yanzu a Jihar Bauchi.
Daga baya sai aka samu rashin jituwa tsakanin Malam Yakubu da Muhammadu Dabo Titi a kan biyan kudin harajin dabbobi, inda aka aika wa Shehu Usman dan Fodio a Sakkwatto. Bayan an yi Shari’a tsakanin su, sai shi Dabo Titi ya bukaci Shehu Usmanu dan Fodio ya mayar da shi karkashin Masarautar Zazzau.
Daga baya sai Shehu ya amince da bukatar Dabo Titi, ya umarce shi da ya koma karkashin masarautar Zazzau. Sai Shehu ya yanke wani bangaren kasar Bauchi da Zazzau inda aka kaddamar da kirkirar Masarautar Lere bayan kammala Yakin Alkalawa a shekarar 1808 inda ta kunshi garuruwa da kabilun Limoro, Sheni, Ziriya, Sanga, Buji, Taura, Ciboko, Gusu, Amagulu, Kayan tare da wasu garuruwan Hausawa da Fulani.
Masarautar Zazzau ta rike kananan masarautu guda 10 (bassal States): Jema’a, Nasarawa, Keffi, Lapai, Kauru, Fatika, Durum. Doma da Lere. masarautar Lere ce kadai aka bata dama ta mallaki Tambura 12 a cikin wadannan masarautu.
Shehu ya bai wa Dabo Titi dama ya ci gaba da zama a Toro. Malam Yakubu bai ji dadin hakan ba, inda ya umarci Dabo Titi ya fice daga yankin, a lokacin da yaki ficewa, sai Malam Yakubu ya zo da mayaka zuwa Kudancin Toro inda ya kwace Ribina. Da Dabo Titi ya kai kara wajen Sarkin Zazzau Malam Musa, sannan ya nemi izini a kan daukar fansa, sai Sarki Malam Musa ya umarce shi da ya tafi Kudu maso Yamma domin a samu maslaha. Sai Dabo Titi ya koma tare da jama’arsa zuwa inda ‘yan kabilar Limoro ke zaune, ya kafa garinsa mai suna Kunka.
Tun lokacin da aka kirkiri masarautar a karkashin Zazzau a shekarar 1808, Lere na gudanar da sarauta ce ta gado. Sarkin Lere na farko Muhammadu Dabo Titi yana da ‘ya’ya hudu, Yaji, Idris, Mamman da Abdulkadir. Biyu daga cikinsu sun gaje shi bayan rasuwarsa a 1830.
Daga nan ne aka ci gaba da gadon sarautar tsakanin ‘ya’yan wadannan ‘ya’yan Dabo Titin guda biyu har zuwa sarkin Lere na 13 na yanzu Birgediya Janaral Abubakar Garba Muhammed wanda jika ne ga Idris.
kasar Lere a farko kamar yadda Shehu ya bayar tana girma sosai.Ta Gabas ta kai wani waje da ake kira Inkel.Ta Kudu ta kai Rafin Dillimi da Farar Gada a garin Jos. Ta Arewa kuma ta kai garin Riruwai da ke Jihar Kano.Ta Yamma kuma ta yi iyaka da rafin Lere da ake kira rafin karami.
Sai suka fara yaduwa waje daban daban saboda yawansu har lokacin da aka kafa wajen da take a yanzu a shekarar 1870 wanda Sarkin Lere Muhammadu dankaka ya jagoranta. Hakan ya faru ne bayan Sarkin Ningi dan Maje da rundunarsa sun kai farmaki garin Masherengi, gabas da garin Saminaka na yanzu, inda shi Sarkin Lere dankaka yake zaune. Ningawa sun sami nasarar kona garin cikin dare. Sai Sarkin Lere dankaka ya bar Masherengi ya zo ya kafa garin Lere a inda take a yanzu.
Sarkin Lere na biyu Idris Murabus ya kafa garinsa a kusa da dutsen Gurba. Shi kuma dan uwansa Sarkin Lere Mamman ya zabi wajen da ake kira Liyanga wanda da ke kusa da Domawa na yanzu.
Sarakunan Lere:
1. Sarkin Lere Muhammadu Dabo Titi (1808-1830)
2. Sarkin Lere Idris Murabus dan Dabo Titi (1830-1847)
3. Sarkin Lere Aliyu na 1 dan Idris Murabus (1847-1850)
4. Sarkin Lee Mamman dan Dabo Titi (1850-1856)
5. Sarkin Lere Muhammadu dankaka dan Idris Murabus (1857-1905)
Bayan turawan mulkin mallaka sun amshe masarautun Arewa a shekarar 1903, suka canza tsarin masarautu zuwa gundumomi da larduna. Sai aka mayar da Lere matsayin gunduma a shekarar 1905 a lokacin Sarki Muhammadu dankaka.
– Sarkin Lere Muhammadu dankaka dan Idris Murabus (1905-1907)
1. Sarkin Lere Abdullahi dan Muhammadu dankaka (1907-1912)
2. Sarkin Lere Abubakar dan Muhammadu dankaka (1912-1915)
3. Sai kuma Sarkin Lere Abdullahi dan Muhammadu ya sake dawowa (1915-1918)
4. Sai kuma Barden Lere ya yi riko (1918-1920)
A tsakanin 1907 zuwa 1918 lokacin sarautar Sarkin Zazzau Aliyu dan Sidi, an tsige Sarkin Lere Abdullahi da Sarkin Lere Abubakar. Sarkin Ruwan Zazzau Sallau, dan Galadiman Zazzau Abbas da dan uwansa Walin Zazzau Halliru suka ci gaba da lura da masarautar har 1920. A 1920 sai aka nada Walin Zazzau Halliru a matsayin Hakimin Lere a1924. Daga nan kuma sai sarautar hakimcin Lere ta ci gaba:
1. Walin Zazzau Umaru (1925-1946)
2. Dallatun Zazzau Muhammadu (1946-1951)
3. Walin Zazzau Umaru (1951-1968)
4. Makaman Zazzau karami, Alhaji Halliru (1968-1986)
Hakanan kuma a shekarar 1920 lokacin da aka nada Sarkin Lere Aliyu Mai’Itu a matsayin Dagacin Lere, wadannan mutanen sun mulki Lere a matsayin Dagatai:
1. Sarkin Lere Aliyu Mai’Itu (1920-1924)
2. Sarkin Lere Musa Ladan (1924-1927)
3. Sarkin Lere Muhammadu Mijinyawa (1927-1942)
4. Sarkin Lere Alhaji Muhammadu Sani (1942-1980)
5. Sarkin Lere Alhaji Umaru Muhammad (1980-1986)
Mayar da sarautar ga asalin magada
A shekarar 1986 ne aka sake samun sauyi lokacin da aka nada Sarkin Lere Alhaji Umaru Muhammad wanda a lokacin shi ne dagaci, ya zama Hakimi bayan ya gaji Makaman Zazzau Alhaji Halliru wanda ya rasu a shekarar.
daga darajar Masarautar Lere
A 27 ga watan Disamba, shekarar 2000 ne aka daga martabar masarautar Lere daga gunduma zuwa masarauta mai daraja ta uku.Sannan kuma Gwamna Ahmed Mohammed Makarfi ya kara daga darajar Masarautar Lere zuwa masarauta mai daraja ta biyu a ranar 9 ga watan Maris, shekarar 2007.
A lokacin da Sarkin Lere Alhaji Umaru Muhammed ya rasu a shekarar 2011, sai kaninsa Sarkin Lere na yanzu Birigediya Janar Garba Abubakar Muhammed ya gaje shi, inda aka ba shi sandar mulki a ranar 9 ga watan Maris, shekarar 2011.
Daga littafin Lere Chronicle wanda Abdullahi Muhammed Doki da Ismaila Umaru Lere suka rubuta.