Wannan ita ce dangantakarsa wacce babu sabani a kai, kamar yadda kuma ba a yi sabani ba wajen cewa Adnan daya ne daga cikin zuriyar Annabi Isma’il (AS) ba. Wato ke nan dangartakar Annabi (SAW) ta hadu da ta Annabi Isma’il dan Annabi Ibrahim (AS). Haka nan Annabi (SAW) mahaifinsa da mahaifiyarsa tushensu daya ne. Kabilar Annabi (SAW) ita ce Kuraishawa wadda aka tabbatar tana da daukaka da girman sha’ani da asali abin tinkaho da tataccen matsayi a tsakanin Larabawa. Dukan mazan wannan kabila shugabanni ne madaukaka a zamaninsu. Kusayyu sunansa Zaidu shi ne farkon wanda ya fara kula da kiyaye Ka’aba, mabudinta na hannunsa yana budewa ga wanda ya so don shi ne wanda ya saukar da Kuraishawa a cikin Makka, ya kasance kafin wannan duk a warwatse suke a geffanta cudanye da wasu kabilu shi ne wanda ya kirkiro ba da abin sha da abinci ga masu zuwa ziyarar Ka’aba kuma ya gina wani daki kusa da Ka’aba inda ake tarurruka na shawarwari da su daura aure, ba a yanke wata shawara sai a cikinsa. Tutar yaki da zaben jagoran yaki duk a hannunsa suke, mutum ne mai yalwataccen tunani, ma’abucin iya zartar da magana a cikin mutanensa da iyalinsa. Wannan aiki nasa a haka sauran zuriyarsa suka yi ta gada daya bayan daya, har ya zo kan Hashim, sunansa na asali Amru, Kakan Annabi (SAW) na biyu daga baya ta koma cikin ’ya’yansa Abdulmuddalib ya gaje shi a wannan aiki har zuwan Musulunci. Hashim ya auri Kakar Annabi (SAW) ta biyu Salma ’yar Amru dan Addiyi a Yasriba (Madina) kan hanyarsa ta zuwa Sham ya dan zauna tare da ita sannan ya wuce Sham a lokacin tana da cikin Abdulmuddalib bai dawo gare ta ba ya rasu a Gaza kasar Falasdinu. Salma ta haifi da a cikin danginta aka sanya masa suna Shaibah don furfurar da aka haife shi da ita, kuma dangin mahaifinsa ba su san da shi ba sai da ya kai shekara bakwai. Sai dan uwan mahaifinsa da ake kira Muddalib ya ji labari ya je ya taho da shi Makka sai mutane suka zaci bawa ne ya sayo sai suke kiransa bawan Muddalib wato Abdulmuddalib, sai sunan na asali Shaibah ya bace. Abdulmuddalib ya girma a Makka wurin dangin mahaifinsa, mutum ne kyakkyawa ya samu daukaka a cikin Kuraishawa wadda wani bai samu ba kafin shi. Shi ne shugaba kuma jagoran ayarin kasuwanci, mutum ne mai yawan kyauta har ta kasance yana ajiye abinci ga miskinai da tsuntsaye da dabbobi, shi ya sa aka kara hako rijiyar Zamzam bayan kasa ta cike ta. A lokacinsa ne aka yi waki’ar giwa da Abraha ya zo da mutanensa suka kawo hari Ka’aba don su rusa ta Allah Ya aiko musu da tsuntsaye suka hallaka su, a lokacin saura wata biyu a haifi Manzon Allah (SAW).
Mahaifin Manzon Allah (SAW) Abdullahi shi ne mafi kyautatuwar ’ya’yan Abdulmuddalib da rangwamensu, kuma mafi soyuwa a wurin Abdulmuddalib, amma duk da wannan kauna kadan ya rage ya yanka Abdullahi a matsayin hadaya ga Allah, saboda a lokacin hakar rijiyar zamzam Kuraishawa sun yi jayayya da shi wadda ta sa har ya yi alwashi idan Allah Ya ba shi ’ya’ya goma maza zai yanka daya. Da suka kai cikarsu sai ya yi musu kuri’a kuma kuri’ar ta fada kan Abdullahi inda ya tafi da shi Ka’aba zai yanka shi, amma sai Kuraishawa suka hana musamman ’yan uwansa na kusa, a kan haka har suka fanshe shi da rakuma 100.
Bayan wannan sai Abdulmudallib ya zaba wa Abdullahi Aminatu ’yar Wahabi don ya aura. Amina ta kasance mafificiyar matan Kuraishawa ta bangaren daukaka da matsayi, mahaifinta shi ne shugaban kabilarsa ta Zuhrata. An daura aurensu kuma suka tare a nan Makka. A takaice Manzon Allah (SAW) ya fito ne daga mahaifa biyu tsarkaka, masu daraja da daukaka.Wannan wata baiwa ce daga Allah. An samo Hadisi daga Wasilah binu Aska’i ya ce: Annabi (SAW) ya ce, “Hakika Allah ya fifita Annabi Isma’il a cikin ’ya’yan Annabi Ibrahim kuma ya fifita Kinana daga ’ya’yan Annabi Isma’il kuma ya fifita Kuraishawa a cikin ’ya’yan Kinanah kuma ya fifita ’ya’yan Hashim a cikin Kuraishawa. Ni kuma ya fifita ni daga cikin ’ya’yan Hashim.” (Muslim ya ruwaito shi).
Haka nan Hirakal Sarkin Rum ya tambayi Abu Sufyan wanda yake adawa da Annabi (SAW) a lokacin kafin ya musulunta, game da dangantakar Annabi (SAW), sai ya ce: “Lallai dangantakarsa mai kyau ce a cikinmu, sai Hirakal ya ce: “Hakika haka ne dukan sauran Annabawa ana aiko su ne daga mafi kyan dangantakar mutanensu.” (Bukhari ya ruwaito).
Darasi na Shida: Sunansa da nasabarsa Sunan Annabinmu Muhammad (SAW). Amma ya zo a cikin wasu hadisai da yawa cewa ana kiransa da wasu sunaye daban, wadanda shi da kansa ya ambace su. Jubair Ibn Mud’im ya ruwaito cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ni ne Muhammad, kuma ni ne Mahi wanda Allah Yake shafe kafirci da ni, kuma ni ne Hashir wanda ake tashin mutane (a karkashinsa) Ranar Lahira, kuma ni ne Akib wadda babu wani Annabi a bayana.” Muslim ne ya ruwaito wannan Hadisi. Haka kuma Abdullahi bin Kais ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ambaci sunayensa gare mu ya ce: “Ni ne Muhammad, ni ne Ahmad, ni ne Mukaffa. Kuma ni ne Nabiyyut-Taubati, kuma Nabiyyur-Rahmati.” (Imam Ahmad ne ya ruwaito). Jabir dan Abdullahi (RA) ya ce Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ni ne Ahmad, kuma ni ne Muhammad, kuma ni ne Hashir, kuma ni ne Mahi wanda Allah Ya shafe kafirci da ni, idan Ranar Alkiyama ta zo, tutar godiya tana tare da ni, na kasance ni ne Shugaban Manzanni kuma ma’abocin cetonsu.” Haka nan cikin Alkur’ani an ambaci Annabi (SAW) da sunayen da suke nuna girman darajarsa da alherin da zuwansa ya kawo wa duniya da girman matsayinsa a wajen Allah (SWT). Ga misalai:
“Muhammadu Manzon Allah ne. Kuma wadannan da suke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu, kana ganinsu suna masu ruku’i suna masu sujuda, suna neman falala daga Ubangijinsu da yardarsa… ” (Fathi:29).
“Muhammadu bai kasance uban kowa ba daga mazanku, kuma amma shi ya kasance Manzon Allah kuma cikamakin Annabawa. Kuma Allah Ya kasance Masani ga komai.” (Ahzab:40).
“Kuma a lokacin da Isa dan Maryamu ya ce Ya Ba ni Isra’ila! Lallai ni, Manzon Allah ne zuwa gare ku. Mai gaskata abin da ke gaba gare ni na Attaura, kuma mai bayar da bushara ga wani manzo da ke zuwa a bayana, sunansa Ahmad (Masha yabo). To, a lokacin da ya je musu da hujjoji sai suka ce wannan sihiri ne bayyananne.” (Saff:6).
Kamar yadda muka ambata, Annabi (SAW) yana da NASABA tsarkakakkiya mai nuna kyawun asalinsa da kuma tabbatar da cewa yana da tushe daga gidan manyan mutane masu daraja da ke kaiwa har zuwa ga Annabi Isma’il (AS) da Baban Annabawa Annabi Ibrahim (AS). Ana jera sunan Annabi Muhammad (SAW) da nasabarsa kamar haka; Muhammad dan Abdullahi dan Abdulmuddalib dan Abdu Manaf dan Kusayyu dan Kilabu dan Murratu dan Ka’abu dan Lu’ayyu dan Galib dan Fihr (Kuraishi), shi ne dan Malik dan Nadhru (Kais) dan Kinanata dan Khuzaimata dan Mudrikata (Amir) dan Ilyas dan Muzar dan Nizar dan Ma’ad dan Adnan. Shi kuma Adnan kaka ne na 20 ga Manzon Allah (SAW), kuma karshen nasaba mafi inganci da ake da ita ke nan a tsarin nasabar Manzon Allah (SAW).
Za a iya samun Aliyu Muhammad Sa’id, Gamawa
Ta +2348023893141
Email: [email protected]