✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tarihi: Yadda Cristiano Ronaldo ya ci kwallo 800

Da kwallo biyu da ya zura, yanzu Ronaldo yana kwallo 801 ne ke nan.

A ranar Alhamis ne Manchester United ta doke Arsenal da ci uku da biyu, inda Cristiano Ronaldo ya ci kwallo biyu.

Da kwallo biyu da ya zura, yanzu Ronaldo yana kwallo 801 ne ke nan a tarihin taka ledarsa a kasa da kungiyoyi.

Ronaldo ya ci kwallo 11 ke nan a wasa 16 da ya buga tun dawowarsa Manchester United a kakar bana.

A kungiyoyin da ya buga, ya zura kwallo 685, sannan ya ci kwallo 115 a kasarsa ta Portugal.

Ronaldo has scored the most goals at Real Madrid with 450.

Yadda ya zura kwallo 801

Ya fi cin kwallo a Real Madrid, inda yake da kwallo 450.

Sai Manchester United inda yake da jimillar kwallo 115, kasarsa Portugal inda ya ci kwallo 115.

A kungiyar Juventus, ya ci kwallo 101, sai kungiyarsa ta farko, Sporting CP inda yake da kwallo biyar.