✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tarihi 5 da Ronaldo ya kafa a wasan Portugal da Liechtensen

Ronaldo ya jefa kwallo cikon ta 60 a bugun tazara a tarihi.

Cristiano Ronaldo ya buga wa Portugal wasa na 197, ya kuma ci kwallo biyu a wasan neman shiga Euro 2024, bayan doke Liechtensen 4-0.

Mai shekara 38, shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a tawaga a tarihi mai 120 kawo yanzu.

Ya fara yi wa Portugal tamaula a 2003, wanda a Gasar Kofin Duniya a Qatar a 2022 ya zama na farko da ya zura kwallo a kowacce gasa biyar a Kofin duniyar.

Minti takwas da fara wasa Portugal ta ci kwallo ta hannun Joao Cancelo, minti biyu da komawa zagaye na biyu Bernardo Silva ya kara na biyu.

Sai Cristiano Ronaldo ya ci na uku a bugun fenariti, sannan ya kara na hudu na biyu da ya zura a raga a wasan.

Kwallo ta biyu da Ronaldo ya jefa a wasan a bugun tazara, ita ce cikon ta 60 da ya jefa a irin wannan salo a tarihi.

Haka kuma, tun daga shekarar 2004 kawo yanzu, babu shekarar da tauraron bai jefa wa kasarsa kwallo akalla daya ba.

Ronaldo bai tsaya nan ba, a wasan dai ya ci wa Portugal kwallon cikon ta 100 a duk gasanni wadanda ba na sada zumunta ba ne.

A Gasar Kofin Duniya a Qatar da Ronaldo ya buga, shi ne ya yi kan-kan-kan da Bader Al-Mutawa, wanda ya yi wa Kuwait fafatawa 196.

Ronaldo ya yi kafada da dan kwallon Kuwait a yawan buga wa tawaga tamaula a wasan da Morocco ta fitar da Portugal a zagayen quarter finals.

Mai Ballon d’Or biyar ya yi zaman benci a Qatar a Portugal, sai dai sabon koci, Roberto Martinez ya gayyaci tsohon dan wasan Real Madrid da Juventus.

Ronaldo ya koma taka leda a gasar kwallon kafa ta Saudi Arabia a Al Nassr a watan Janairu, bayan da ya raba gari da Manchester United.