✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Goma Sha Tara: Fiffikon fadar Allah Madaukaki cewa: “Kada ka yi tsammanin wadanda aka kashe ta hanyar daukaka kalmar Allah matattu ne. A’a…

Babi na Goma Sha Tara:

Fiffikon fadar Allah Madaukaki cewa: “Kada ka yi tsammanin wadanda aka kashe ta hanyar daukaka kalmar Allah matattu ne. A’a rayayyu ne a wurin Ubangijinsu ana azurta su. Suna masu farin ciki da abin da Allah Ya ba su daga falalarSa. Kuma suna masu bushara ga wadanda ba su iske su ba daga bayansu cewa: “Babu wani tsoro a kansu kuma su ba masu bakin ciki ba ne. Suna masu bushara da wata ni’ima daga wajen Allah da fifitawa. Hakika Allah ba Ya tozarta ladar mumminai.” (k:3:169-171).

504. An karbo daga Isma’il dan Abdullahi ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Is’hak dan Abdullahi dan Abu dalha daga Anas dan Malik (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya yi addu’a a kan wadanda suka kashe mutanen rijiyar Ma’unah har safiya talatin. Bisa kabilar Ri’il da Zakwan Usayyah da ta saba wa Allah da ManzonSa.” Anas ya ce, “An saukar da wata aya cikin Alkur’ani game da mutanen rijiyar Ma’unah wadda muke karantawa daga baya aka shafe ta da cewa: “Ku isar wa jama’armu lallai mu, mun iske Ubangijinmu Ya yarda da mu, kuma mun yarda da shi.”

505. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Amru cewa, ya ji Jabir dan Abdullahi (RA) yana cewa: “Mutane sun dafa giya suka sha suka bugu (maye) a ranar Yakin Uhudu, sa’an nan aka kashe masu shahada,” sai aka tambayi Sufiyan cewa: “A karshen wannan wuni? Ya ce, “Wannan ba ya daga cikin Hadisin.”

 Babi na Ashirin:  Inuwar Mala’iku ga wanda ya yi shahada:

506. An karbo daga Sadakat dan Fadal ya ce: “dan Uyaina ya ba mu labari ya ce: “Na ji Muhammad dan Munkadir yana cewa: “Lallai shi ya ji Jabir dan Abdullahi yana cewa: “An zo da babana zuwa ga Annabi (SAW) lokacin da aka sanya shi gaba gare shi (Annabi). Sai na tafi domin in bude fuskarsa sai jama’ata suka hana ni. Sai (Annabi) ya ji kukan mutuwa aka ce ’yar Amru ce, ko aka ce, ’yar uwar Amru. Ya ce: “Don me kike kuka? Ko ya ce, “Kada ki yi kuka,” Mala’iku ba za su gushe ba suna inuwantar da shi da fika-fikansu.” Sai na ce da Sadakat: “Shin Mala’iku na inuwantar da shi har lokacin bisine shi? Ya ce, “Ina tsammanin ya fade shi (haka).”

 

Babi na Ashirin da daya: Burin mujahidi da a ce zai komo duniya bayan shahada:

507. An karbo daga Muhammad dan Bashar ya ce: “Gundar ya ba mu labari ya ce, Shu’abah ya ba mu labari ya ce: “Na ji Anas dan Malik (RA) ya ce: Daga Annabi (SAW) ya ce: “Babu wanda zai shiga Aljanna ya yi burin ya komo duniya, saboda abin da ya iske na alheri face wanda ya yi mutuwar shahada. Zai yi burin ya komo duniya a kashe shi sau goma wajen daukaka kalmar Allah saboda abin da ya gani na karramawa (matsayi).” 

 

Babi na Ashirin da Biyu: Aljanna tana karkashin haduwar takubba ne:

508. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Mu’awiyya dan Amru ya ba mu labari ya ce, Abu Is’hak ya ba mu labari daga Musa dan Ukubah daga Salim abu Nadar bawan Umar dan Ubaidullahi ya kasance marubuci ya ce: “Abdullahi dan Abu Awfah (RA) ya rubuta zuwa gare shi cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Hakika Aljanna ta kasance a karkashin inuwar takubba ne.” Uwaisi ya karbo daga dan Abu Zinad daga Musa dan Ukuba.