✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ficewar Nijar, Mali da Burkina Faso Barazana ce —ECOWAS

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) ta bayyana yunkurin ficewar kasashen Nijar da Chadi da Burkina faso daga cikinta a matsayin mummunan barazana ga…

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) ta bayyana yunkurin ficewar kasashen Nijar da Chadi da Burkina faso daga cikinta a matsayin mummunan barazana ga harkokin tsaron yankin.

Kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na ECOWAS, Abdel-Fatau Musah ne ya bayyana hakan a yayin wani zama mai taken: “Dakile Matsaloli Ta Hanyar Hadin Gwiwar  Masu Ruwa da Tsaki a Fannin Tsaro A Yankin da Abin Ya Shafa” wanda kungiyar Tarayyar Turai tare da hadin gwiwar Cibiyar Yaki da Ta’addanci (NCTC) suka shirya a Abuja ranar Laraba.

A watan Janairu ne dai kasashen uku da sojoji ke jagoranta suka sanar da ficewarsu daga ECOWAS.

Sun ce sun fita daga ECOWAS din ne saboda zargin kungiyar da zama barazana ga ’yan kasashensu.

Musah ya ce: “ Ficewar mambobin ECOWAS uku su kuma kulla kawancem Sahel ya dagula yaki da ta’addanci a yankin Afirka ta yamma.

“Matsayar ECOWAS a nan ita ce muna bukatar wadannan kasashen su dawo a ci gaba da tafiya tare, kuma za mu yi duk abin da ya dace domin dawo da su.

“Muna buƙatar su, taken wannan taro namu shi ne haɗin gwiwa, haɗin gwiwa da abokan arziki domin yakar babban abokin gaba wato ta’addanci.”

Kwamishinan na ECOWAS ya ce, tuni ta’addanci ke barazana ga kasashen uku, yana mai cewa “Idan ba mu hada kai mun yaki wannan ba, dukkanmu za mu shiga matsala.”

Ya ce, ’yan ta’adda sun mamaye kusan rabin kasar Burkina Faso, akwai fargabar cewa Afirka da ma duniya baki daya za su iya shiga gagarumar matsala idan har aka bar ’yan ta’adda suka samu wurin zama mai kyau na kai hare-hare a Yammacin Afirka.

Ya ce, a yanzu haka kungiyar ECOWAS na shirin gudanar da wani taro domin tunkarar matsalolin da suka dabaibaye kasashen uku, da hanyoyin magance su.