Jami’o’in kasar Birtaniya na shirin fara daukar daliban Najeriya masu shaidar jarabawar kammala sakandare ta NECO.
Shugaban hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO), Farfesa Ibrahim Wushishi, ya ce Jami’ar Lead da Jami’ar Birmingham City da ke kasar Birtaniya sun tuntubi hukumar kan jarabawar da take shiryawa.
Ya ce jami’o’in sun fara tunanin bai wa daliban Najeriya gurbin karatu da sakamakon jarabawarsu ta NECO.
A fahimtarsa, hakan na nuni da amincewa da ingancin sakamakon jarabawar NECO ne a idanun manyan jami’o’in ciki da wajen Najeriya.
- Majalisa amince wa Tinubu ciyo bashin $500m don sayen mitocin lantarki
- Manyan ’yan ta’adda sun kashe juna a Katsina
Farfesa Wushishi ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da ’yan jarida a Abuja ranar Laraba.
Ya ce NECO ta cika sharudan Jami’ar Birmingham City, kuma a halin yanzu suna aiki tukuru kan ganin sun sami cika sharudan jami’ar Lead.