✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tarayyar Turai za ta hukunta kamfanin Google

Nan da ‘yar kwanaki ne Tarayyar Turai wato EU za ta sanar da irin matakin da za ta dauka akan kamfanin Google bisa tuhumar nuna…

Nan da ‘yar kwanaki ne Tarayyar Turai wato EU za ta sanar da irin matakin da za ta dauka akan kamfanin Google bisa tuhumar nuna son kai wajen bai wa masu amfani da intanet dama su yi amfani da manhajarsa cikin sauri fiye da sauran kamfanoni da ke gogayya da shi, bayan wani bincike ya tabbatar da hakan.

Kwamishina mai kula da sashen gasar tallata hajar kamfanoni ta EU, Magrethe bestager ce za ta sanar da matakin a nan gaba kadan. Hakan kuwa yana nuni ne da irin yadda aka ba wa korafe-korafen da kamfanoni ke yi akan Google din.
Kamfanin na Google dai yana mamaye kasuwar intanet a nahiyar Turai da kaso 90 cikin 100. Sai dai kamfanin ya musanta zargin. Amma a shekaranjiya Laraba hannun jarin kamfanin ya dan samu koma baya.