Tsoffin gwamnonin Zamfara hudu sun yi wata ganawar sirri da nufin lalubo mafita daga matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa a jihar.
Tsofaffin gwamnonin sun hada Sanata Ahmed Sani Yarima, Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar da kuma Karamnin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle.
Wakilimu ya gano cewa an yi taron ne a gidan Matawalle da ke Abuja a cikin dare, inda suka shafe sama da da awa uku suna tattaunawa.
Duk da cewa ba a bayyana ainihin abin da taron ya tattauna ba, wata majiya mai kusanci da taron ta shaida mana cewa, zaman ya mayar hankali ne kan hanyoyin kawo karshe matsalar tsaro a Zamfara, da zummar ganin harkokin tattalin arziki da al’amuran yau da kullum da bangaren more rayuwa sun bunkasa.
Majiyar ta ce Matawalle ya bayyana wa sauran tsoffin gwamnonin aniyarsa ta yin aiki tare da su domin kawo karshen ayyukan ’yan bindaga a jihar Zamfara.
Zaman tsoffin gwamnonin ya kuma tattauna kan matsalolin jam’iyyar APC da kuma bukatar farfado da ita a jiharsu.
Tabarbarewar sha’anin tsaro na tsawon shekaru sakamakon ayyukan ’yan bindiga ya durkusar da harkokin yau da kullum musmman na tattalin arziki a jihar Zamfara.