’Yan sanda sun yi nasarar ragargazar masu satar mutane a kauyen Kuriga da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna.
’Yan sandan sun hallaka biyu daga cikin ’yan ta’addar da suka dauki lokaci suna addabar al’ummar yankin, bayan wani ba ta kashi a tsakaninsu.
Yayin farmakin, ’yan sanda sun yi nasarar karbe muggan makamai daga hannun ’yan bindigar da ake zargin da hannunsu wurin sace daliban Makarantar Kuriga a kwanakain baya.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan , ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
- Rashin Tsaro: Tsoffin gwamnonin Zamfara sun yi taron sirri
- Shugaban kasar Iran ya rasu a hatsarin jirgin sama
Ya ce, ’yan sandan sun samu wannan nasarace bayan al’ummar yankin sun kai rahoto game da harin da ’yan bindiga suka kai wa manoma a gefen kauyen Kuriga.
“Jami’an tsaron sun yi artabu da ’yan ta’addan a wani kazamin musayar wuta, inda suka yi nasarar hallaka biyu daga cikin masu ’yan bindigar.
“Jami’an sun yi nasarar kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu da alburusai kunshi 17 ,” in ji shi.
Gwamnan jihar, Sanata Uba Sani, ya yaba wa kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ali Audu Dabigi, tare da jami’ansa, bisa kwazon da suke nunawa.
Gwamnan ya kuma bukace da sauran jami’an tsaro a yankin da su ci gaba da bibiyar masu aikata miyagun laifuka tare da tabbatar da tarwatsa su gaba daya.