Tankin ajiyar ruwan asibitin Kuchigoro da aka fi sani da Asibitin Shugaba Buhari da ke Unguwar Kuchigoro a kan titin zuwa filin jirgin saman Abuja ya fashe bayan wata shida da kaddamar da shi, inda ya raunata masu masu juna biyu.
Asibitin wanda aka inganta shi da kayyayakin zamani don karbar haihuwa da kwantar da majinyata tankin adana ruwansa ya fashe ne da misalin karfe 11 na ranar 14 ga Yuli lokacin da mata masu juna biyu ke yin awo daf da tankin inda ruwan da ya yi ambaliya ya kwashi mata da malaman asibiti ya raunata su.
Asibitin wanda tsohon asibitin sha-ka-tafi ne, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne da kansa ya kaddamar da shi bayan an daukaka darajarsa zuwa karamin asibitin karbar haihuwa da kwantar da marasa lafiya a ranar 10 ga Janairun bana, inda mazauna yankin suka yi ta yabo ganin za su huta da kashe kudi don zuwa manyan asibitoci ko na kudi.
Lokacin da Aminiya ta ziyarci asibitin, ta ga yadda tankin karfe da ya fado kan na kasa na roba ya tarwatsa su yayin suke cike da ruwa kuma suka yi ambaliya.
Wakilinmu ya lura kuma da yadda na’urar samar da wutar lantarki mai aiki da hasken rana da ke saman tankin ta samu lahani, inda wayoyinta suka tsinke suka daina aiki ga na’urar sanyaya magunguna na asibitin.
Mutanen da abin ya faru a gabansu sun yi mamakin fashewar tankin bayan wata shida kacal da kaddamar da asibitin, alhali wasu tankunan samar da ruwa na gwamnati da na ’yan kasuwa a gefe da aka kafa turakunsu shekaru da dama ba su fashe ba.
Wata mata da ta sha da kyar bayan fashewar tankin wacce ta nemi a sakaya sunanta wadda ta je awo a asibitin, ta ce fashewar tankunan ruwan ta firgita kowa, ruwa ya kwashe su ya yi gaba da su, sannan ya yi musu rauni duk da suna da juna biyu, bayan asarar kayayyaki kamar su wayoyin hannu da sauransu da suka yi. Ma’aikatan asibitin sun ce ba za su iya yin magana ba don ba a ba su izini.
Asibtin dai na hadin gwiwa ne a tsakanin Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da Ma’aikatar Birnin Tarayya, Abuja da karamar Hukumar Birnin Abuja (AMAC).
Mutanen da Aminiya ta tattauna da su, sun ce abin yana da bata rai, kuma sun yi zargin ba a yi aiki mai inganci ba, alhali asibitin haihuwa yana da bukatar ruwa don tsabtace shi a koyaushe. Sun ce akwai tankunan adana ruwa da aka yi a wasu asibitoci da suka kai shekaru barkatai amma ko yoyo ba sa yi balle su fashe.
Sarkin Kucigoro, Cif Ibrahim Wambi ya shaida wa Aminiya cewa ya yi tafiya, sai ya dawo ya gane wa idonsa abin da ya faru kafin ya ce uffan.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa Hukumar AMAC ta umarci dan kwnagilar ya koma ya gyara aikin sa, kuma ya yarda zai koma ya gyara barnar da fahsewar tankunan ruwan suka jawo.