✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tankar mai ta yi bindiga ’yan sa’oi bayan gobarar Kasuwar Katako ta Bodija

Wata tanka makare da bakin mai ta yi bindiga, sa'o'i kadan bayan gobarar da ta lakume Kasuwar ’Yan Katako ta Bodija da ke Jihar Oyo.

Wata tanka makare da bakin mai ta yi bindiga, sa’o’i kadan bayan gobarar da ta lakume Kasuwar Katako ta Bodija da ke Jihar Oyo.

Tankar ta kama da wuta ne kimanin sa’a biyu bayan ziyarar da Gwamna Seyi Makinde na jihar ya kai wa ’yan Kasuwar Bodija ziyarar jaje, kan gobarar da ta yi musu mummunar barna.

Hukumar tsaron ta Karamar Hukumar Oluyole  ta jihar ta ce, kafin motar ta yi bindiga, wasu mazauna yankin da suka lura wuta tana ci a karkashin motar sun ankarar da direban.

Ganin haka ne direban ya yi sauri ya sauka daga motar, a yayin da sauran mutanen da ke wurin kuma ya yi ta kansa.

Daga bisani motar ta bindigar, inda man da take dauke da shi ya tsiyaye a cikin magudana, wuta ta rika ci na tsawon lokaci.

A yayin ziyarar gwamnan, ya ba wa ’yan kasuwar da suka yi asara a gobarar tallafin Naira miliyan 25, sannan ya yi alkawarin Majailsar Karamar Hukumar Ibadan ta Arewa za ta sake hanyoyin da ke cikin kasuwar.