✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tankar mai ta yi bindiga a Anambra  

Ba a samu asarar rai ba a hatsarin.

Tankar mai dauke da man fetur ta yi bindiga a mahadar Hukumar Kula da Shige da Fice da ke birnin Awka a Jihar Anambra. 

Ko da yake, ba a samu asarar rai ba yayin da mutane biyu da ke cikin motar ne kadai lamarin ya rutsa da su.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:50 na safiyar ranar Talata, inda gobarar ta laso wata babbar mota mara rajista.

Wani ganau ya bayyana cewa, kwatsam tankar ta kama da wuta bayan faduwarta, lamarin da ya sa direban da kwandastan suka tsere.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura na Kasa (FRSC) reshen jihar, Adeoye Irelewuyi, ya alakanta musabbabin hatsarin da gudun wuce kima.

Ya gargadi masu ababen hawa da su daina gudun wuce kima da kuma kiyaye ka’idojin tuki.

Ya ce, “Wani direban tankar mai dauke da man fetur da ba a san ko wanene ba ya yi wani dan karamin hatsari a mahadar hanyar Awka zuwa Enugu a yau 15 ga Nuwamba, 2022 da misalin karfe 06:50 na safe.

“Maza biyu hatsarin ya shafa. Amma babu wanda ya mutu kuma babu wanda ya jikkata. An kubutar da mutanen biyu ba tare da sun ji rauni ba.

“Jami’an ceto na FRSC na Anambra sun kula da zirga-zirgar ababen hawa yayin da jami’an kashe gobara kuma suka rika kai kawo wajen kashe gobarar.”

Shugaban Hukumar Kashe Gobara na jihar, Injiniya Martin Agbili, ya ce ba a samu asarar rai ba a gobarar, sai dai ya ce direban tankar da kwandastansa sun gudu daga wurin jim kadan bayan faruwar lamarin.

%d bloggers like this: