Akalla mutum biyu ne suka mutu, wasu da dama suka jikkata a lokacin da wata tankar mai ta yi bindiga a yankin Ogidi na Karamar Hukumar Idemili ta Arewa a Jihar Anambra.
Gobarar ta tashi bayan motar ta yi bindiga ta kuma kona motoci akalla 14 da sauran dukiyoyi na miliyoyin Naira a kusa da kasuwar Ogidi.
– ’Yan Boko Haram 190 sun sake mika wuya a Borno
– ‘Hayar masu garkuwa da ni aka dauko daga Zamfara’
Wani ganau ya shaida mana cewa wutar ta kama ne bayan faduwar da tankar man ta yi.
Ya ce bayan faduwarta motar sai man da take dauke da shi ya zube wanda hakan ya sa wuta ta tashi nan take.
Wani mazaunin unguwar mai suna Uche Michael, wanda ya gane wa idonsa yadda lamarin ya faru ya ce tankar na tsaye ne lokacin da wata babbar mota ta kwace ta afka mata.
Ya ce “Motocin alfarma da shagunan da ke wurin duk sun kama da wuta bayan tashin wutar wadda take ta ci sosai ta yadda masu kashe gobara sun sha wahala kafin shawo kanta.”
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, Injiniya Martin Agbili, ya ce mutum biyu sun mutu sannan an yi asarar dukiya mai tarin yawa.
Kazalika, ya ce zuwan jami’an hukumar a kan lokaci ya hana wutar ta kama wasu gine-gine da ke yankin, ciki har da kasuwar yankin.
“Nan take muka aike da motoci biyar na kashe wuta a wurin da motar ta fadi, amma sai da aka dauki awanni kafin a kashe wutar.
“Motocin da suka kone na mutanen yankin ne. Mun gode wa Allah kan yadda aka shawo kan wutar,” a cewarsa.
Kakakin ’yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ’yan sanda sun isa wurin don hana bata-gari cin karensu babu babba.