✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tankar mai makare da fetur ta yi hatsari a hanyar Abuja

Tsiyayar man da motar da tauko ya sa mzauna guje-gujen neman tsira.

Wata tankar mai makare da fetur ta yi hatsari a kan Babbar Hanyar Maraba zuwa Abuja.

Ganin man da motar ta dauko yana tsiyaya babu kakkautawa a kan titi ya sa mazauna da masu kantuna da ke kusa da hanyar gudun tsira da rayukansu.

A hannu guda kuma, wasu bata-gari sun rika amfani da yanayin wurin satar kaya daga kantunan da masu su suka tsere.

Wani ganau, Hassan Abdulkareem, ya ce tankar man ta kwace ne a yayin da direbanta ke kokarin kauce wa wani rami a daidai mahadar Mopol Junction da ke Mararaba a Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.

“Abin ya faru ne ranar Litinin da dare, kuma kasancewa motar ta dauko fetur, sai man da ke tsiyaya daga motar ya rika gangarawa zuwa shaguna da gidajen da ke yankin.

“Hakan ta sa yawancin masu kantuna da mazauna yankin kwashe kayansu saboda tsoron tashin wuta daga man da ke tsiyaya,” inji shi.

Ya kara da cewa tuni jami’an kwana-kwana tare babbar hanyar domin shawo kan abin da ka iya biyo baya.

%d bloggers like this: