Wata tankar mai cike da fetur ta yi bindiga a cikin wani gidan mai da ke garin Dutse, hedikwatar Jihar Jigawa.
A safiyar Juma’a ne kakakin ’yan sanda a Jihar Jigawa, SP Shiisu Adamu, ya sanar cewa lamarin ya faru ne a gidan mai na Shakkato da ke kan hanyar Kiyawa.
Hakan na zuwa ne yayin da aka samu karuwar fashewar tankoki dauke da man fetur a Najeriya, wanda mafi muninsu a baya-bayan nan ya yi ajalin sama da mutum 100 a Jihar Neja.
Ko a shekarar da ta gabata, irin haka ya faru a Jihar Jigawa, inda sama damutum 100 suka rasu.
- Seaman Abbas da Hussaina: An dakatar da shirin Brekete Family Hausa
- An ɗaure zawarawa a gidan yari kan aikata zina
Da yake tabbatar cewa abin ya auku ne a ranar Alhamis, SP Shiisu Adamu ya bayyana cewa, amma ba a samu asarar rai ba.
Ya ce binciken farko ya nuna tankar man fetur din ta kama da wuta ne a yayin da motar take kokarin sauke man da ta dauko a gidan man.
“Kafin kiftawa da Bismillah wutar ta yi girma fiye da misali inda nan take aka kira hukumar kashe gobara, ta gaggauta zuwa tare da nasarar shawo kan lamarin.”