Akalla mutum tara ne suka mutu, yayin da wasu 40 suka jikkata lokacin da wata tankar gas ta yi bindiga a yankin Boksburg na birnin Johannesburg a Kasar Afrika Ta Kudu.
Tankar wadda ke makare da gas ta makale a karkashin wata gada, lamarin da ya sanya ta bindiga kafin a ciro ta.
- EFCC ta yi gwanjon kadarorin su Diezani a kasuwa
- A karon farko, an ba Bahaushe Kwamishina a Kuros Riba
Kakakin Hukumar Bayar da Agajin yankin, William Ntladi, ya ce tuni aka kira jami’an hukumar kashe gobara zuwa yankin.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar, inda hukumomi a yankin ke ci gaba da kai dauki don ceto mutanen da lamarin ya rutsa da su.
An ruwaito tankar na dauke da lita 60,000 ta gas, yayin da lamarin ya faru.
Ministan Lafiya Kasar, Phaahla, ya ce tankar ta yi bindiga kusa da wani asibiti, lamarin da ya sanya rabin sashen kula da hatsari na asibitin ya kone.