✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tanim Yari ne Gwarzon gasar karatun Alkura’ani ta kasa ta kungiyar Izala

Tanim A. Yari  daga Jihar Neja ne ya zama gwarzon shekara na gasar karatun Alkura’ani mai girma na kasa, karo na 21 da kungiyar Jama’atu…

Tanim A. Yari  daga Jihar Neja ne ya zama gwarzon shekara na gasar karatun Alkura’ani mai girma na kasa, karo na 21 da kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa ta shirya a birnin Yola, a fadar gwamnatin Jihar Adamawa a makon da ya gabata. A yayin da Mas’ud Idris Gital daga Jihar Bauchi ya zo na biyu, Misbahu Abubakar daga Jihar Kebbi ya zo na uku, Muhammad Auwal daga Jihar Gombe yazo na hudu, Nuhu Adam Ibrahim daga Jihar Kaduna kuma yazo na biyar.

Da yake jawabi a wajen rufe gasar, shugaban majalisar malamai na kasa na kungiyar Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa a duk inda katarun Alkura’ani ya sauka, alheri ya sauka a wajen. Ya ce don haka   kungiyar ta tashi tsaye wajen karantar da Alkura’ani a kowanne lungu da sako na Nijeriya da kasashen waje. Ya ce karatun Alkurani yana budewa dan’adam basira,  don haka ya yi kira ga al’ummar musulmi su rika karatun Alkura’ani saboda alherin dake tattare da yin haka. 

Har’ila yau ya yi kira ga al’ummar musulmi su tashi tsayen wajen koyan  harshen larabci domin su fahimci karatun Alkura’ani. Ya ce  babu harshen da ya kai harshen larabci fusaha da cikakken  bayani, kamar harshen larabci.  

Daga nan ya yabawa gwamnan jihar Adamawa kan irin goyan baya da tallabin da ya bayar wajen  gudanar da wannan gasar karatun Alkura’ani. A wajen rufe wannan gasa dai, an raba kyaututtukan motoci da baburan hawa da akwatunan tilbijin da kudade ga wadanda suka zamo zakaru a  gasar.