Gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal ya soke wasu ayyuka da gwamnatin tsohon Gwamna Sanata Aliyu Wamakko ta bayar a Jihar.
Zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar ya soke kwangilar ayyukka biyar na Gwamnatin Wamakko da aka yi watsi da su.
- Dole ce ta sa makiyaya suka fara amfani da AK-47 –Gwamnan Bauchi
- Har yanzu El-Rufai bai fahimci batun matsalar rashin tsaro ba —Ganduje
- Dalibin aji hudu ya lashe gasar musabakar Al-Qur’ani a Kebbi
- CBN na mayar da ’yan Arewa saniyar ware a harkokin kudade – ACF
Hudu daga cikinsu da dan kwangila ya watsar a Asibitin Murtala Muhammad sun hada da ginin karin dakunan jinya biyu da fitar da wurare a cikin asibitin da gina gidajen ma’aikata 47.
Akwai kuma aikin kammala ayyukka na musamman da suka kunshi dakin tiyata, dakin ajiye gawa da wurin wanki dasauransu.
Tambuwal ya kuma soke kwangilar gina Asibitin Wamakko da aka ba da kwangila tun a shekarar 2013, lokacin Sanata Wamakko na gwamna.
Tambuwal zai gina asibiti mai gado 608
Majalisar Zartarwar ta kuma bayar da ayyukkan gina asibitin zamani mai daukar gadaje 608 a garin Binji, da gina dakunan kwana a Makarantar Koyon Aikin Kiyon Lafiya ta Sarki Abdurrahman da ke Gwadabawa, da wasu manyan dakunan kwana biyu a Kwalejin Shehu Shagari a Sokoto.
Bayan taron da Gwamna Tambuwal ya jagoranta, Kwamishinan Ilmi Mai Zurfi Farfesa Bashir Garba, ya ce an ware biliyan N2.7 don aikin gina asibitin da za a kammala aikinsa cikin wata 17.
Aikin kwalejin malamai kuma zai lakume miliyan N524, makarantar kiyon lafiya kuma miliyan N523, sannan duk za a kammala ne cikin wata tara.
A nasa bangaren, Kwamishinan Lafiya Dakta Ali Muhammad Inname ya ce an soke kwangilar asibitin Murtala ne saboda watsi da aikin da dankwangilar ya yi.
Ya ce za a bi ka’idodin doka kafin sake ba da kwangilar ga wasu kamfanonin da suka shirya.
Kwamishinan ya kara da cewa Asibitin Wamakko kuma an jima da bayar da aikin ga wani sabon kamfani.